Inyamuri nike son ya zama shugaban kasa a 2023, Obasanjo
- Yayinda ake cigaba da shirye-shiryen zaben 2023, tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Igbo ya zama shugaban kasa
- Obasanjo ya bayyana hakan ranar Alhamis, 10 ga Maris a gidansa dake Abeikuta lokaci Mazi Sam Ohuabunwa ya ziyarcesa
- Mazi Sam Ohuabunwa na cikin wadanda suka bayyana takara a zaben shugaban kasa a 2023
Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya jaddada cewa ba karamin dadi zai ji ba idan dan kabilar Igbo ya zama Shugaban kasa bayan Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.
Obasanjo ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata a hada kan yan Najeriya ta hanyar baiwa dan yankin kudu maso gabas shugabancin Najeriya.
Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 10 ga Maris, yayinda dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Mazi Sam Ohuabunwa, ya kai masa ziyara gidansa dake Abeokuta, TheSun ta ruwaito.
Yace:
"Bayan hadin kan kasar nan da zai haifar, na yi imanin baiwa yan kudu maso gabas na da kwazo da ilmi. Hakan zai taimaka wajen samar da arziki da yaki da talaucin da suka addabi Najeriya."
Ya bayyanawa Ohuabunwa cewa neman kujeran shugaban kasa abune mai wuya amma yaji dadin yana nema.
Da ace EFCC na aikinta yadda ya kamata, da wasu masu neman kujerar Buhari suna kurkuku - Obasanjo
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Asabar, 5 ga watan Maris, ya ce da ace hukumar EFCC na aikinta yadda ya kamata toh da ya kamata ace wasu masu neman takarar kujerar shugaban kasar Najeriya a 2023 suna a gidan yari.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a yayin wani taro na bikin cikarsa shekaru 85 a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.
Tsohon shugaban kasar ya ce koda dai masu neman takarar shugaban kasa da dama sun ziyarce shi domin neman goyon bayansa, shi bai tsayar da wani dan takara da zai marawa baya ba.
Asali: Legit.ng