Borno: Sojoji Sun Gasa Wa Ƴan Ta'adda Aya A Hannu, Sun Kashe 10 Sun Ƙwato Bindigu Masu Harbo Jiragen Sama
- Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwato bindigogin harbo jiragen sama guda 4 a hannun ‘yan bindiga yayin da suka kai samame tsakanin ranar 24 ga watan Fabrairu da 10 ga watan Maris
- Shugabannin rundunar tsaro ne suka bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai inda suka saki takarda wacce ta yi bayani dalla-dalla akan yadda suke yakar Boko Haram da ISWAP
- Sun samu wadannan tarin nasarorin ne cikin makwanni 2 a kauyakun da ke arewa maso gabashin Najeriya kamar karamar hukumar Gwoza, Damboa da Biu duk a cikin Jihar Borno
Jihar Borno - Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar kwato bindigogin harbo jirgin sama yayin da ta kai samame tsakanin ranar 24 ga watan Fabrairu da 10 ga watan Maris.
An samu bayanai ne a wata tattaunawar da manema labarai suka yi da shugabannin harkokin labaran soji kan ayyukan sojin Najeriya a yankin, The Punch ta ruwaito.
Takardar da suka saki ta yi bayani dalla-dalla akan nasarorin su
Kamar yadda suka saki takarda inda ta bayyana cewa:
“Rundunar Operation Hadin Kai cikin makwanni biyu ta samu tarin nasarori masu yawa wurin yakar mayakan Boko Haram da ISWAP tare da sauran ‘yan ta’adda.
“Sakamakon ayyukan rundunar a wasu wurare da ke arewa maso gabas kamar tsaunin Mandara, Tudun Kwatara, Kauyen Fadagwe a karamar hukumar Gwoza, yankin Timbuktu, kauyen Buk da ke Karamar hukumar Damboa da Mallam Fatori da ke karamar hukumar Biu duk a Jihar Borno.
“Dagewar da rundunar ta yi wurin yakar mayakan ISWAP da ke tsaunin Mandara a karamar hukumar Gwoza da kuma Timbuktu da ke karamar hukumar Damboa ya ja ta halaka ‘yan ta’adda 10. Sojojin sun kwato bindigogi 4 kirar AA, babura 10, abu mai fashewa guda daya, MOWAG APC guda daya, motar yaki daya mai bindigu 122, bindigu kirar AK-47 guda 4 da wasu ababen fashewa guda 5.”
A wani yankin jihar, sun halaka ‘yan ta’adda 2 sannan sun kwace makamai da dama a wurin su
The Punch ta ruwaito yadda takardar ta ci gaba da bayyana yadda sojojin suka yi karon batta da mayakan ISWAP a kauyen Debiro-Shaffa da ke karamar hukumar Hawul inda suka halaka wasu ‘yan ta’adda 2 inda suka kwace bindiga kirar AK-47, magazin 3 da sauran miyagun makamai.
Yanzu haka ‘yan Boko Haram da ISWAP suna ci gaba da mika wuyan su ga sojoji a wurare daban-daban, wanda yanzu haka ‘yan ta’adda 174 da iyalansu sun mika wuya.
Cikin su akwai maza manya guda 43, mata 58 da yara 73 daga kauyakun da ke kusa da Bama da Dikwa a Jihar Borno.
Tuni aka samar wa tubabbun ‘yan ta’addan da iyalan su mafaka.
Boko Haram sun dawo Chibok, sun kashe mutane, sun ƙona gidaje masu yawa
A wani labarin daban, kun ji cewa a kalla fararen hula uku ne suka riga mu gidan gaskiya a yayin da wasu da ake zargin yan Boko Haram ne suka kai hari a kauye da ke karamar hukumar Chibok a Jihar Borno da yammacin ranar Jumma'a.
Kungiyar yan ta'addan sun afka kauyen Kautikari da ke kusa da gari Chibok misalin karfe 4 na yamma, suna harbe-harbe ba kakkautawa kuma suka kona gidaje da dama a cewar majiyoyi na tsaro, Daily Trust ta ruwaito.
A cewar majiyar, maharan sun iso ne a cikin motocci guda biyar dauke da bindiga mai harbo jiragen yaki kuma suka shigo cikin sauki ba tare da an nemi taka musu birki ba.
Asali: Legit.ng