Labari Da Ɗuminsa: Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa, ACF, Ta Yi Babban Rashi

Labari Da Ɗuminsa: Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa, ACF, Ta Yi Babban Rashi

  • Allah ya yi wa Sakataren Kungiyar Tuntuba ta Arewa, ACF, na kasa, Emmanuel Yawe rasuwa yana da shekaru 65
  • Marigayin ya rasu ne cikin barcinsa a gidansa da ke babban birnin tarayya a Abuja kamar yadda yarsa Talata, ta tabbatar
  • Talatu Yawe ta ce mahaifin nata ya yi rashin lafiya a yan kwanakin baya amma ya ji sauki kawai dai ya kwanta barci ranar Alhamis amma ba a tashi da shi Juma'a ba

FCT, Abuja - Babban Sakataren watsa labarai na Kungiyar Tuntuba ta Arewa, ACF, Emmanuel Yawe ya riga mu gidan gaskiya.

Daily Trust ta rahoto cewa Yawe, mai shekaru 65 ya rasu ne a barcinsa a safiyar ranar Juma'a a Abuja.

Labari Da Ɗuminsa: Ƙungiyar Tuntuba Ta Arewa, ACF, ta yi babban rashi
ACF: Allah ya yi wa Emmanuel Yawe rasuwa. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Aikin da ya yi na karshe shine a ranar Alhamis inda ya fitar da sanarwa a madadin ACF na ta'aziyya ga mutanen Benue kan rasuwar Hon. B.A. Bacha, tsohon kakakin majalisar wakilai na tarayya.

Kara karanta wannan

Jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya tsakiyar daji saboda mai ya kare

Talatu Yawe, 'yar marigayin ta tabbatar da rasuwarsa

Yar Yawe, Talatu Yawe ta tabbatar da rasuwarsa ga Daily Trust.

Ta ce mahifinta ya rika zuwa asibiti a watannin da suka shude amma lafiyarsa kalau kuma yana gina a ranar Alhamis.

"Duk da cewa ya yi rashin lafiya, lafiyarsa kalau a jiya Alhamis. Bai tashi ba daga barci a safen yau Juma'a," in ji ta.

Marigayi Yawe ya bar matar sure da yara hudu.

Mahaifiyar ɗan majalsa ta rasu awa 24 bayan raba wa matan da mazajensu suka rasu kuɗi da kayan abinci

A wani rahoton, mahaifiyar Dan Majalisar Wakilai na Tarayya kuma tsohon dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar All Progressives Grand Alliance, APGA, a Jihar Anambra, Chuma Umeoji, ta rasu, rahoon The Punch.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyar da ya rika karbar albashin N15, 000 ya rasu

Mahaifiyar dan majalisar, Ngozi Umeoji, ta rasu ne a ranar Lahadi, a kalla awa 24 bayan ta raba wa matan da mazajensu suka rasu shinkafa, kudi da kayan abinci a garinsu a Ezinifite, karamar hukumar Aguata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: