Da duminsa: Jam'iyyar APC ta yiwa INEC raddi kan wasikar da ta aike mata
- Jam'iyyar APC ta yi wa hukumar INEC raddi bisa wasikar da ta aiko na cewa bata bi ka'ida ba
- Kakakin kwamitin rikon kwaryan APC ya bayyanawa manema labarai cewa ba sai jam'iyyar ta sanar da INEC ba
- Hukumar INEC tace doka ta tanadi a sanar da ita akalla kwanaki 21 kafin a gudanar da wani taron gangami
Jam'iyyar All Progressives Congress APC ta yi watsi da wasikar da hukumar zabe ta kasa INEC ta aike mata na cewa tana bukatar a sanar da ita kwanaki 21 akalla kafin taron gangamin da aka shirya ranar 26 ga Mairs, 2022.
Shugaban matasan APC kuma kakakin kwamitin rikon kwarya, Barista Ismail Ahmed, ya bayyana hakan ga manema labarai ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja.
Yace jam'iyyar tuni ta sanar da hukumar niyyar taron gangaminta na ranar 26 ga Febrairu kuma abinda ake bukata yanzu shine fadawa INEC ta dage taron amma ba sabon sanarwa ba.
Akan maganar da INEC tayi cewa Shugaban jam'iyyar bai sanya hannu kan wasikar ba, Isma'il bai yi tsokaci ba.
Shugaban jam'iyya bai sanya hannu ba
Mun kawo muku rahoton cewa hukumar zabe ta kasa INEC ta yi watsi da wasikar gayyata zuwa taron majalisar zartaswa na gaggawa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC.
Hukumar INEC ta bayyana cewa ta yi watsi da takardar ne saboda bata ga sanya hannun Shugaban jam'iyya, da na Sakatare AkpanUduohehe ba.
INEC, a wasikar da ta aike ranar 9 ga Maris, 2022 kuma Sakatarenta, Rose Oriaran Anthony, ta rattafa hannu, hukumar ta ce APC ta saba ka'idar Article 1.1.3 na dokokin ayyukan jam'iyyun siyasa.
INEC ta kara da cewa bisa sashe na 82(1) na dokar zabe, akwai bukatar a sanar da ita ana saura kwanaki 21 akalla kafin wani babban taro, ko ganawa don maja da zaben sabbin shugabanninta.
Asali: Legit.ng