Yankin Yarbawa zai balle daga Najeriya ba tare da bindiga ba, Sunday Igboho

Yankin Yarbawa zai balle daga Najeriya ba tare da bindiga ba, Sunday Igboho

  • Alamu sun fara nuna Sunday Igboho ya horu, domin kuwa ya ce sam babu batun fada a lamarin neman ballewa
  • Ya ce kasar Yarbawa za ta kafu ko da kuwa ba a dauki makami ba, don haka ya ce tattaunawa ne mafita akan haka
  • Ya bayyana haka ne a furucinsa na farko tun bayan da aka sako shi daga magarkama a jamhuriyar Benin a makon jiya

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, dan awaren Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya ce fafutukar neman cin gashin kai na yankin Yarabawa za ta yi nasara.

Igboho, wanda aka saka kwanan nan daga magarkamar jamhuriyar Benin, ya ce 'yan awaren Yarbawa za su tabbatar da kafuwar kasar Yarbawa ba tare da harba ko da harsashi daya ba.

Kara karanta wannan

2023: Wani Farfesan Najeriya Ya Yunƙuro, Zai Nemi Kujerar Buhari a Ƙarkshin Jam'iyyar APC

Igboho ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da lauyansa, Cif Yomi Aliyyu (SAN) ya fitar a madadinsa, domin yabawa wasu shugabannin Yarbawa da suka hada da Farfesa Banji Akintoye, Farfesa Wale Adeniran da Cif Dele Momodu wajen ciro shi daga magarkama.

Dan awaren Yarbawa ya magantu
Yakin Yarbawa sai ya balle daga Najeriya ba tare mun dauki bindiga ba, Sunday Igboho | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya kuma yabawa Aliyu kan yadda ya kula da kararsa a kan hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ba tare da karbar kobo ba.

Igboho da DSS suka kai farmaki gidansa a ranar 1 ga watan Yuli, 2021, ya bukaci magoya bayansa da duk masu fafutukar kafa kasar Yarbawa da su yi amfani da hanyar tattaunawa da lumana don cimma burinsu.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Igboho Oosa, ya mika godiyarsa ga duk wadanda suke goyon bayansa, musamman shugabanninsa, Farfesa Akintoye da Farfesa Wale Adeniran, da daukacin ‘yan Najeriya, musamman mutanensa na Ilana Oodua da sauran kungiyoyin 'yan aware.

Kara karanta wannan

Babu maganar janye yajin-aiki, kungiyar ASUU ta gindayawa Gwamnatin Najeriya sharadi

"Ya ci gaba da wa'azi game da kaucewa yaki, ganin abubuwan da ke faruwa a Ukraine da wasu sassan lardin Inyamurai a Najeriya."

Ya kuma yi kira ga kowa da kowa, musamman ’yan uwansa na gida da waje da su rungumi akidar tattaunawa don neman yancin kansu ba tare da kara zafi ga halin da Najeriya ke ciki ba.

Wannan furuci shi ne na baya-bayan nan daga Igboho tun bayan da hukumomin Jamhuriyar Benin suka sako shi a ranar Litinin, inji rahoton Channels Tv.

Kungiyar Yarbawa ta sa baki, Jamhuriyar Benin ta saki dan awaren Yarbawa Sunday Igboho

A wani labarin, jaridar Punch ta rahoto cewa, Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta saki dan awaren Yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Ighoho bayan doguwar tsarewa da ya sha.

Hadin kan Yarbawa a kungiyoyin rajin kare hakkin Yarabawa ta Ilana Omo Oodua Worldwide ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Shugaban APC na kasa: Magoya baya sun hada N10m don siyawa zabin Buhari fam

Sanarwar wadda mai magana da yawun Ilana Omo Oodua, Mista Maxwell Adeleye, ya fitar, mai taken, ‘Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta Saki Dan rajin kare al’ummar Yarabawa, Sunday Adeyemo Ighoho ga shugaban Yarbawa, Banji Akintoye; Masanin harshen Faransanci, Adeniran'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.