'Yan Sanda Sun Gurfanar da Tsohuwar Matar Fani-Kayode, Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama A Kotu

'Yan Sanda Sun Gurfanar da Tsohuwar Matar Fani-Kayode, Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama A Kotu

  • A ranar Alhamis ‘yan sanda suka gurfanar da Precious Chikwendu, tsohuwar matar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode bisa zargin ta da laifuka 5 na yanar gizo
  • An gurfanar da ita gaban alkalin babbar kotun tarayya da ke Abuja, Justice Obiora Egwuatu inda duk ta musanta laifukan da ake zargin ta aikata
  • Bayan nan ne lauyan me kara ya bukaci a garkame ta a gidan gyaran halin Kuje wanda lauyan ta ya ki amincewa da hakan inda yace bata saba sharadin beli ba

FCT, Abuja - ‘Yan sanda sun gurfanar da Precious Chikwendu, tsohuwar matan tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode kan laifuka masu alaka da intanet, Daily Trust ta ruwaito.

An gurfanar da Chikwendu gaban alkali Obiora Egwuatu da ke babbar kotun tarayya, Abuja, inda ta musanta duk laifukan da aka zarge ta da aikatawa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan sanda sun mutu yayin da motar tawagar ministocin Buhari ta yi hadari

'Yan Sanda Sun Gurfanar da Tsohuwar Matar Fani-Kayode, Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama A Kotu
'Yan Sanda Sun Gurfanar da Tsohuwar Matar Fani-Kayode Kan Zargin Laifi Ta Yanar Gizo. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Bayan kin amsa laifukan, lauyan mai kara, Mr Victor ya nemi kotu ta sanya ranar da za a ci gaba da sauraron kara sannan ta nemi kotu ta garkame Chikwendu a gidan gyaran halin Kuje.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, kamar yadda The Punch ta ruwaito, ya kamata a garkame ta har sai an kammala sauraron karar kuma an yi hukunci akan lamarin.

Lauyan Chikwendu ya nuna rashin amincewarsa da batun garkame ta

Sai dai a bangaren Chikwendu, lauyan da ke kare ta, Alex Ejesieme, SAN ya nuna rashin amincewarsa akan wannan bukatar inda ya ce bukatar ta ba shi mamaki.

Kamar yadda ya ce:

“Ina mamaki kan yadda wancan lauyan ya ke mika wannan bukatar ga kotu.”

Babban lauyan ya sanar da kotu cewa ya nemi belin ta a wurin ‘yan sanda kuma har an amince masa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsohon dan wasan kwallon Najeriya ya yanki jiki ya fadi matacce a Jos

Ejesieme ya ce bukatar a rike Chikwendu a gidan gyaran hali ba abar dubawa bace musamman idan aka kalli cewa bata saba wani sharadin belin da ‘yan sanda suka gindaya mata ba.

Yadda jami'an DSS 5 suka taimaka min na yi garkuwa da kwastoma na, Wanda ake Zargi

A wani labarin, kun ji cewa wani Akeem Ogunnubi mai shekaru 42 ya bayyana yadda ya yi garkuwa da wani dan kasuwa a Sabo mai suna Bola cikin ranakun karshen mako, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Olawale Olokode dama ya bayar da labari yayin tasa keyar mutumin da ake zargi cewa wasu maza dauke da bindigogi sun sace wani dan canji har cikin ofishinsa a ranar 30 ga watan Disamban 2021 da misalin karfe 5:30 da yamma.

Wanda lamarin ya faru da shi kamar yadda Olukode ya shaida ya ce sun zarce da shi daji ne sannan suka bukaci kudin fansa kafin su sake shi, a nan su ka yi masa kwacen N204,000 sannan suka tsere suka bar shi a wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164