Jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya tsakiyar daji saboda mai ya kare
- Mai ya karewa sabon jirgin kasan Legas zuwa Ibadan da shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar kwanaki
- Fasinjoji sun fito daga cikin jirgin da ya tsaya a tsakiyar daji suna kokarin ganewa idanunsu abinda ya faru
- Yan Najeriya a kafafen ra'ayi sada zumunta sun tofa albarkatun bakinsu kan wannan lamari
Legas - Jirgin kasa mai jigilar fasinjojo daga jihar Legas zuwa Ibadan, a ranar Alhamis, ya tsaya tsakiyar dajin sakamakon karewar mai a cikinsa.
Wani ma'abocin manhajar Tuwita, @shollychei ya saki bidiyon yadda fasinjoji suka fito daga cikin jirgin don ganin ikon Allah.
Yayinda wasu fasinjojin sun zauna kan layin dogon, saura na hira a tsaye.
Amma daya baya ya dawo yace jirgin ya tashi, zasu cigaba da tafiya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wannan abu ya auku yayinda yan Najeriya ke fama da tsadar man fetur a fadin tarayya.
Birane irinsu Legas, Abuja, Fatakwal da ire-irensu sun jijjigu da dogayen layukan mai wanda ya kai ga har kwana ake a gidajen mai.
Ga lokacin da ake zuba mai;
Martanin yan Najeriya:
Abubakar Fana Aminu:
Kai wani abin, almara sai kasata Nigeria Ubangiji Allah ya kawomana shuwagabanni masu jin tausayimmu ameen ya Rabbi
Umar Aliyu:
Du da matsalar tsaron da yake damin mu amma jubi wani abin kunya wai jirgin gwamnati babu mai a cikin sa
Zakari D Bocho:
Babbar magana karamci Mai harda jirgin kasa a Nigeria Allah ya kiyaye gaba Kar ace Mai yakarewa jirgin Buhari a sararin samaniya, manja zezama ja kenan
Aliyu Suleiman:
Wannan ai sakaci da ganganci yakamata a hukunta duk wanda suka jawo wannan sakacin don kiyaye rayuka da dukiyoyin al'umma.
Jibrin Usman Bakori:
Subar shege nan kawai su kama gaban su, idan kuma za su iya su tura shi zuwa gari wajen ƴanbunburutu a zuba.
Bashir Muhammad Tagana:
Wannan ba dai dai ne ba,
Wasane da rayukan Al'umma, yadda qasar nan ya dagule ga harakar tsaro.
Asali: Legit.ng