DSS ta kama shugabannin kananan hukumomi 2 a Kano kan daukar nauyin dabar siyasa
- Hukumar DSS ta yi ram da shugabannin kananan hukumomin Gwarzo da na birni da kewaye na jihar Kano
- An kama Bashir Kutama da Faizu Alfindiki kan zargin daukar nauyin dabar siyasa a jihar wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka hudu da jikkata wasu da dama
- Hasashe sun nuna cewa shugabannin biyu na hararar kujerar gwamnan jihar
Kano - Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama Bashir Kutama da Faizu Alfindiki, shugaban kananan hukumomin Gwarzo da na birni da kewaye, kan zargin amfani da yan daba a jihar.
Ci gaban na zuwa ne bayan wani karo da aka yi kwanan nan tsakanin magoya bayan yan siyasar biyu wadanda ake ganin suna hararar kujerar gwamnan Kano, Daily Trust ta rahoto.
The Cable ta rahoto cewa an kashe mutane hudu, yayin da wasu da dama suka jikkata a yayin rantsar da jami’an APC na yankin Kano ta kudu a Rano.
Wata majiya a ofishin DSS reshen Kano, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da kamun shugabannin kananan hukumomin biyu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
“Eh, sun kama Mista Faizu Alfindiki, shugaban karamar hukumar birni da kewaye da Bashir Abdullahi Kutama, shugaban karamar hukumar Gwarzo, kan zargin daukar nauyin manyan yan daban siyasa a jihar, inda suka kai hare-hare da kuma kisa.
“DSS ta kuma sanya Khalid Ishaq Diso, shugaban karamar hukumar Gwale, cikin wannan zargin, yayin da jami’an tsaro suka kuma kama wani hadimin gwamna duk a kan zargin.
“Hukumar DSS ta fara gagarumin yunkuri domin duba mummunan lamarin, wanda idan aka bari ya ci gaba, yana iya sanya Kano ta kama da wuta tunma kafin a fara zaben 2023.”
An tasa keyar dan adawan Ganduje, Dan Bilki Kwamanda, gidan gyaran hali
A wani labarin, mun ji cewa an gurfanar da shi a kotu ne kan zargin batanci da sharri wa gwamna Ganduje, rahoton DailyTrust.
Rahotanni sun nuna cewa Danbilki ya zargi Ganduje da laifin bada cin hanci ga Mai Mala Buni da mambobin kwamitinsa don tabbatar da cewa Abdullahi Abbas, ya zama Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano.
Alkalin kotun, Aminu Magashi, a ranar Talata ya bada umurnin tasa keyar Kwamanda zuwa gidan yari bayan watsi da bukatar belin da lauyansa yayi.
Asali: Legit.ng