Jami'in ɗan sanda ya yanke jiki ya fadi ya mutu nan take a wurin Jana'izar Kakansa

Jami'in ɗan sanda ya yanke jiki ya fadi ya mutu nan take a wurin Jana'izar Kakansa

  • Wani insufektan yan sanda a jihar Bayelsa ya yanke jiki ya faɗi, kuma Allah ya masa rasuwa a wurin bikin jana'izar kakarsa da ta mutu
  • Insufekta Michael Tamitihi ya rasa rayuwarsa ne bayan kammala tiƙa rawa domin girmama gawar kakarsa mace a Bayelsa
  • Lamarin ya jefa hukumomin tsaron jihar cikin jimami, wasu sun fara zuwa kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan mamacin

Bayelsa - Wani Insufektan yan sanda, Michael Timitimi, dake aiki a hukumar yan sanda ta jihar Beyelsa, ya yanke jiki ya faɗi, kuma Allah ya masa cikawa nan take.

The Nation ta ruwaito cewa lamarin ya auku a wurin bikin jana'izar kakarsa mace a ƙauyen Igbedi, ƙaramar hukumar Kolokuma/Opokuma.

Mutuwar jami'in ɗan sandan ta jefa hukumomin tsaro da suka haɗa da, yan bijilanti da yan Sa'kai cikin yanayin jimami da tausayi.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun farmaki mataimakin gwamna, rayuka da yawa sun salwanta

Jihar Bayelsa
Jami'an ɗan sanda ya yanke jiki ya fadi ya mutu nan take a wurin Jana'izar Kakansa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ɗan sandan ya yanke jiki ya faɗi kuma ya mutu bayan ya tiƙa rawa cikin koshin lafiya domin girmama marigayya kakarsa.

Yayin da aka kai ziyara hedkwatar wasu hukumomin tsaro, ya nuna ƙarara yadda jami'ai suka shiga kaɗuwa da jimami bayan labarin mutuwar Insufektan yan sanda ya riske su.

Wasu hukumomin tsaro a jihar sun kai ziyarar ta'aziyya

Shugaban ƙungiyar yan Sa'kai na jihar Bayelsa, Honorabul Oyinkuro Lucky Asanakpo, ya jagoranci tawagar shugabannin kungiyarsu zuwa yin ta'aziyya, kamar yadda daily trust ta rahoto.

Shugabannin yan Sa'kai sun kai ziyara har gida domin ta'aziyya da jajantawa iyalan marigayi Insufekta Timitimi, wanda a baya ya yi aiki a rundunar su ta yan Sa'akai.

A wani labarin na daban kuma Dakarun yan sanda sun kama daruruwan yan bindiga da yan fashi a jihar Kaduna

Kara karanta wannan

Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Katsina, shugaba ya bindige yaransa har Lahira

Rundunar yan sanda ta jihar Kaduna tace ta samu nasarar yin ram da yan binduga 200, yan fashi 20 a faɗin jihar.

Kakakin yan sandan ya kuma bayyana cewa hukumar ta kwato makamai da yawa duk a tsakanin watan Janairu zuwa Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262