Yayin da yake Kasar Ingila, Buhari ya nada mukami, ya zabi sabon Shugaban HYPREP

Yayin da yake Kasar Ingila, Buhari ya nada mukami, ya zabi sabon Shugaban HYPREP

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin jami’in da zai shugabanci aikin HYPREP
  • Giadom Ferdinand Dumbari zai rike shugabancin HYPREP tun daga yanzu har zuwa shekarar 2026
  • Dr. Giadom Dumbari kwararre ne a bangaren ma’adanai, kuma babban malami ne a jami’ar UNIPORT

FTC, Abuja - Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Giadom Ferdinand Dumbari a matsayin wanda zai kula da aikin HYPREP.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin ma’aikatar muhalli na tarayya a ranar Talata, 8 ga watan Maris 2022. Jaridar nan ta The Cable ta fitar da wannan rahoton.

Dr. Giadom Ferdinand Dumbari zai shafe shekaru hudu yana wannan aiki na magance illar gurbacewar wuri da ake samu a dalilin sinadaran ‘Hydrocarbons’.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: Jami’in ‘Dan Sandan da ya yi bincike kan Abba Kyari ya mutu kwatsam a ofis

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, Ferdinand Dumbari ya samu Digirin farko a ilmin ma’adanan kasa a jami’ar Fatakwal da M. Phil a jami’ar jiha duk a Ribas din.

A wannan jami’ar tarayya da ke Fatakwal ne Giadom Ferdinand Dumbari ya yi PhD a fannin ma’adanai. Malamin jami’ar ya yi rubutu kusan 30 a bangarensa.

Masani a wannan harka

Sabon shugaban na HYPREP ya shafe sama da shekaru 20 yana nazari da bincike a kan hadarin wadannan ‘Hydrocarbons’ da manyan karafuna da sauran sinadarai.

Shugaban kasa
Muhammadu Buhari a taron COP 26 Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A ciken irin nazarin da Ferdinand Dumbari ya yi, ya duba yadda sinadaran suke gurbata Ruwan kasa. Legit.ng ta fahimci hakan ta sa yake ba UNEP shawara tun 2019.

Jaridar Independent ta ce kafin wannan nadin mukami da aka ba shi, Dr. Ferdinand Dumbari kwararren ma’aikaci ne da yake aiki da UNEP a yankin Ogoniland.

Kara karanta wannan

Nadin mukamai ya jawo Lauya ya yi karfin-hali, ya maka Shugaban kasa a gaban Alkali

Bugu da kari, Dr. Dumbari yana cikin kungiyoyin kwararrun masana a kan harkar ma’adanai na kasa. Sannan ya yi aiki da gwamnatin Ribas, NDDC, da kamfanin NDPD.

Ya cancanci ya rike HYPREP

Mun samu labari cewa shugaban na HYPREP ya rike mataimakin shugaba na aikin Shell PER DEC COY, don haka wani abokin aikinsa ya ce lallai ya cancanta.

Wannan jami’in NSCDC da ya yi aiki da shi a Fatakwal ya ce shakka babu Dr. Dumbari ya dace da wannan mukami domin kuwa an dauko wanda ya san bakin zaren.

Wahalar abinci

Yanzu haka mutane su na kukan cewa abinci sun yi tsada a kasar nan. Rahotanni sun nuna cewa muddin ba a dauki mataki ba, abin zai zama wasan yara nan gaba.

Daga cikin abubuwan da za su haddasa mummunan tashin kayan abinci a shekarar nan akwai tsadar takin zamani, yakin Rasha da matsalar rashin tsaro a Arewa.

Kara karanta wannan

Badakalar kwayoyi: Bayan kwanaki 20 a tsare, za a shiga kotu da Abba Kyari da mutum 6

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng