Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Katsina, shugaba ya bindige yaransa har Lahira

Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Katsina, shugaba ya bindige yaransa har Lahira

  • Yan sanda sun fara bincike kan kashe wani bawan Allah da yan bindiga suka yi a karamar hukumar Faskari ta jihar Katsina
  • Rahoto ya nuna cewa rashin bin umarnin yan ta'addan ya haddasa rikici tsakaninsu, nan take shugaba ya harbe yaronsa
  • A halin yanzun yan sanda sun kama mutum biyu da ake zargin suna da hannu a lamarin, kuma sun amsa laifin

Katsina - Hukumar yan sanda reshen jihar Katsina ta fara bincike kan kashe wani ɗan ta'adda da jagoransu ya yi yayin da suka sace wani mutumi.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ɗan ta'addan ya halaka wanda tawagarsu ta yi yunkurin sace wa, hakan ya fusata shugaban su, ya bindige shi nan take.

Ɗan bindigan da aka kashe ya harbe mutumin da suka yi yunkurin sacewa ne bayan ya yi musu gardama ya ƙi bin umarnin tawagarsu na tafiya da shi jeji.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi takansu yayin da jami'an tsaro suka far musu a jihar Katsina

Jihar Katsina
Rikici ya barke tsakanin yan bindiga a Katsina, shugaba ya bindige yaransa har Lahira Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewar hukumar yan sanda, yan bindigan sun farmaki wani kauye a hanyar Dogon Awo- Feeder dake ƙaramar hukumar Faskari a Katsina, ranar Alhamis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoto ya nuna cewa yan bindigan sun kutsa har cikin gidan mutumin, kuma suka yi yinkurin garkuwa da shi. Sun umarci mutumin mai suna, Umar Abdullahi Ankalele, ya biyo su amma ya ƙi.

Ɗaya daga cikin yan ta'addan mai suna, Abdullahi Iliya, ya fusata da gardaman mutumin, nan take ya bindige shi har lahira.

Shugaban tawagar yan bindigan mainsuna Yellow, cikin fushi ya harbe yaronsa saboda kashe mutumin da suka zo sacewa.

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da samun cigaban ranar Talata da daddare.

Yace yanzu haka an kama mutum biyu, Nasiru Mohammed, da Abubakar Iliyasu, da ake zargin suna da alaƙa da kisan mutumin.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun bayyana gaskiyar abin da yasa Fulani Makiyaya suka halaka mutum 7 a Taraba

Ya ce:

"A ranar Alhamis, yan bindiga su Bakwai ɗauke da AK47 suka farmaki gidan Umar Abdullahi Ankalele a wani kauye dake karamar hukumar Faskari suka tafi da shi."
"Garin haka ne, a kokarinsu na tilasta masa bin su, mutumin ya keka she ƙasa, nan take suka bindige shi har lahira. Binciken mu ya gano mutum biyu masu hannu a kisan kuma sun amsa laifin su."
"Sun faɗi yadda lamarin ya faru bisa jagorancin kasurgumin shugaban su Yellow, suka je suka sace mutumin, ɗayan su ya kashe shi saboda ya musu gardama. Nan take shugabansu ya harbe wanda ya kashe mutumin."

A wani labarin kuma Yan bindiga sun sake kai mummunan hari jihar Arewa, sun halaka mutane

Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kauyen jihar Neja a arewacin Najeriya, sun kashe akalla mutum 5 sun sace wasu.

Wani mazaunin ƙauyen da ya samu tsira, ya ce maharan sun farmake su da misalin karfe 10:30 na daren ranar Litinin.

Kara karanta wannan

An Kuma: Yan bindiga sun sake kai mummunan harin jihar Arewa, sun bindige dandazon mutane

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262