Yan sanda sun bayyana daliin da yasa Fulani suka kashe mutum 7 a jihar Taraba
- Hukumar yan sanda reshen jihar Taraba ta tabbatar da mutuwar mutum 7 a wani harin ɗaukar fansa da Fulani makiyaya suka kai
- Kakakin yan sanda, Abdullahi Usman, yace lamarin ya fara ne tun lokacin da aka harbi wani makiyayi a kafa yana tsaka da kiwo a Tor Damisa
- Lamarin da ya fusata Fulanin suka yi yunkurin ɗaukar fansa, kafin jami'an tsaro su dakatar da su, suka kashe mutane
Taraba - Mutum 7 cikinsu har da mace aka tabbatar sun rasa rayukansu yayin da wasu da ake zargin Fulani makiyaya ne suka farmaki ƙauyen Tor Damisa, ƙaramar hukumar Donga, jihar Taraba.
Harin wandaa ake tsammanin na ɗaukar fansa ne ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wasu mayaƙan Tiv sun ji wa makiyayi munanan raunuka yayin da yake kiwon dabbobinsa a yankin kauyen.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abdullahi Usman, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Channels tv, ya ce maharan sun kona gidaje.
A cewarsa, Dakarun soji, yan sanda da yan Bijilanti sun baza komar su ko ina da nufin cafke makasan da kuma gurfanar da su doka ta yi aikinta.
Hukumar yan sanda ta bayyana yadda abun ya faru tun farko
The Nation ta ruwaito Kakakin yan sandan ya ce:
"An ceci wani matashin ɗan Fulani a jeji, ya sha harbin bindiga a ƙafa, ya karye a wurare da yawa a jikinsa, aka kawo shi gaban DPO a can garin Donga. Da aka tambaye shi abin da ya faru, yace mayakan Tiv ne suka harbe shi."
"Bayan gano ɗan jihar Filato ne, aka tuntubi yan uwansa kuma aka damƙa musu shi domin cigaba da kula da lafiyarsa a Asibitin koyarwa na Filato."
"Bayan tafiya da shi, Fulanin dake zaune a kauyen Tur Damisa bisa zargin yan ƙabilar Tiv suka shirya suka kai musu hari."
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
Usman ya ƙara da cewa bayan samun rahoto, jami'an soji, yan sanda da mafarauta suka nufi yankin, amma bisa rashin sa'a kafin isar su Fulanin sun kaddamar da harin.
"Kafin isar jami'an tsaro tuni Fulanin sun kai harin yankin yan ƙabilar Tiv, suka buɗe musu wuta kan mai uwa da wabi, mutum 7 suka mutu."
"Yayin da Dakaru suka isa sun kwantar da hankulan mutane, komai ya dawo dai-dai, yanzu haka sun bazama neman maharan. Yanzu haka komai ya dawo dai-dai."
A wani labarin kuma Wata Mata ta halaka dan uwanta tsoho dan shekara 75 daga fara faɗa, ta yi kokarin boye laifinta
Wata mata ta yi sanadin mutuwar ɗan uwanta na jini kuma tsoho ɗan shekara 75 a duniya bayan samun sabani tsakanin su
Matar ta yi kokarin rufe laifinta ta hanyar shirya cewa kashe kansa ya yi, amma binciken yan sanda ya bankado lamarin.
Asali: Legit.ng