Farji ne mafi muni a jikin mace: Ba fadin Daurawa bane, na Sayyidina Ali ne, inji Dr Mansur Sokoto
- Dr Mansur Sokoto ya yi karin bayani kan maganar Sheikh Daurawa game da abin da wasu mata suka kira kushe halittarsu
- Dr Mansur ya bayyana tushen maganar Daurawa, inda ya kawo bayani daga katafaren littafin tafsiri sananne a duniya
- Dr Mansur ya ce sam ba Daurawa bane ya fara fadin haka, Sayyidina Ali ne ya fadi hakan yayin da yake magana kan gudun duniya
A makon nan ne wasu 'yan sohiyal midiya suka sa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a gaba tun bayan da wani bidiyon karatunsa ya fita, inda ya yi bayani kan gudun duniya da abin da ke cikinta.
Malamin ya yi tsokaci da cewa, mafi munin abu a jikin halittar diya mace ba komai bane fa ce farjinta, lamarin da bai yiwa wasu mata da yawa dadi ba.
Duk da cewa, bidiyon gajere ne, kuma wasu mutane da yawa sun bayyana bukatar a je a kalli cikakken karatun, mata da yawa sun fusata, inda suka ce babu wani karin bayani da suke bukata.
Ga takaitaccen bidiyon Sheikh Daurawa da tsokacin wata mata Rahma Abdulmajid:
Martanin Dr Mansur Sokoto
Gawurtaccen malamin nan mazaunin jihar Sokoto, Dr Mansur Ibrahim Sokoto ya yi karin haske kan wa'azin na Sheikh Darurawa, inda yace ba Daurawa bane ya fara fadin wannan magana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Malamin ya ambaci littafin wani babban malamin tafsirin al-Kur'ani, kuma mabiyin mazahabar Malikiyya dan kasar Andalus, inda malamin ya nakalto wata maganar sahabin Annabi (SAW) kuma surukinsa; Sayyidina Ali (RA) cewa shi ya fadi cewa farjin mace ne mafi muni a jikinta.
Dr Mansur Sokoto dai ya fadi haka ne a shafinsa na Facebook, inda ya rubuta ruwayar maganar Sayyidina Ali (RA) cikin harshen Larabci, kana ya fassara zuwa Hausa.
Ya bayyana inda sahabin ke magana kan jin dadin duniya cewa guda shida ne, yace abinci, abin sha, abin sakawa, abin shaka, abin hawa, sai kuma aure su ne mafi dadi a duniya.
Sayyidina Ali ya yi bayanin kan tushe da kololuwar dadin kowanne daga cikin shidan da ya lissafa, inda yace bai kamata dan Adam ya shiga damuwa saboda su ba.
To, a bayanin batun aure da kuma mace ne Sayyidina Ali (RA) yace:
"Aure kuma jin dadinsa yana wajen mata; wurin fitsari ne yake haduwa da wurin fitsari irin sa. Wallahi duk adon da ka ga mace ta yi, inda ya fi munin ne ake bukata (Farji)".
- Tafsirin Qurtubi (17/255)
Wannan batu na sayyina Ali (RA) daidai yake da abin da Sheikh Daurawa ya fada, don haka Dr Mansur yace ba fadin Daurawa bane, fadin surukin Annabi (SAW) ne
A tsokacin Dr Mansur Sokoto, ya ce ya kamata mutane su lura cewa:
"Wa'azi akan a kiyayi duniya da kushe jin dadinta sanannen abu ne a cikin Alkur'ani da Hadisan Annabi (S) da maganganun magabatan Musulmi. Su kuma shakiyyan mutane neman wurin kushe Annabawa da karantarwarsu suke yi. Mai imani yana nisantar irin wannan tafarki nasu domin ya tsira da imaninsa."
Ga cikakken bayanin Dr Mansur Sokoto:
Hotunan Farfesa Pantami yayin gwajin motar da aka kera a Najeriya mai amfani da wutar lantarki
A wani labarin, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ya yi gwajin wata mota mai amfani da wutar lantarki da aka kera a Najeriya.
Ya yi gwajin motar ne jim kadan bayan da hukumar kula da kera motoci ta kasa (NADDC) ta kawo masa ziyarar aiki a ofishinsa da ke Abuja.
Tagawar ta NADDC tana karkashin jagorancin Darakta Janar na hukumar ne Mista Jelani Aliyu, MFR.
Asali: Legit.ng