Maula da ake tasa mu da ita yasa muke tserewa Abuja, mu sauya lambar waya, 'Yan majalisar Najeriya

Maula da ake tasa mu da ita yasa muke tserewa Abuja, mu sauya lambar waya, 'Yan majalisar Najeriya

  • 'Yan majalisa sun bayyana cewa tsananin maular jama'ar da suka zabe su ne yasa suke tserewa Abuja bayan sun ci zabe kuma su sauya lambar waya
  • Sun sanar da cewa ba su iya yin taruka a dakunan taro na cikin anguwanni saboda yadda jama'a ke takura su da rokarsu kudi
  • A cewarsu, jama'a basu taba tambayarsu ayyukan mazabunsu, sai dai su tambaye su bukatunsu na kansu wanda ba shi ne dalilin zabensu ba

Wasu 'yan majisar dattawa sun yi nuni da rushewar tattalin arzirki a matsayin dalilin bayyananniyar tazara tsakanin 'yan majalisa da mutanen su, inda suka kara da cewa magance matsalolin da ya shafi mutum shi kadai baya daga cikin dalilan da yasa aka zabe su.

Sun koka game da yadda basa iya gudanar da taro a dakin taron cikin anguwa hankali kwance ba tare da mutane sun bukaci a magance musu yunwar cikin su ba, inda suka kara bayyana yadda mutanen mazabar su suke son ganin an raba kudi a irin wannan taron.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan APC a arewa za su siyawa Umahi fam din takara

Maula da ake tasa mu da ita yasa muke tserewa Abuja, mu sauya lambar waya, 'Yan majalisar Najeriya
Maula da ake tasa mu da ita yasa muke tserewa Abuja, mu sauya lambar waya, 'Yan majalisar Najeriya. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Kamar yadda wani dan majalisa dake wakiltar mazabar Yalmatu Deba, Yunusa Abubakar, ya ce, dabi'ar maula da mutane ke wa 'yan majalisar ne yasa wasu daga cikin yan majalisar suka zabi zama a Abuja, Punch ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abubakar ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Gombe, yayin kaddamar da masana'antar arewa maso gabas, wanda Daria Media, tare da tallafin Kungiyar Mac Arthur suka shirya, punch ta ruwaito.

Ya ce, "Hankali da tunanin mutane ya canza. Ban sani ba ko saboda lalacewar tattalin arzirkin Najeriya da duniya ne, yasa mutane ke fama da yunwa, sannan kowa na neman kudi, wanda suke ganin masu mulki sun fi kowa samun kudi.
"Idan aka gabatar da irin wadannan taruka, mutane basa zuwa don zurfafa shi ko kawo cigaba ga al'umma, sai dai dan amfanin kansu. Kafin ka shirya irin wannan taron, dole kazo da jaka cike da kudi don ka raba musu."

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama masu laifi 462, sun kuma kwato makamai

Ya bayyana yadda mutane ke ikirarin cewa 'yan majalisa basa zuwa gida, "hakan na nufin ya jima baya tura musu kudi, ko ya zo bai basu kudi ba, za su ce bai zo ba.
"Wani abun ban tsaro shi ne, duk wani dan majalisan dake son kusanci sai yayi zalama, saboda ko dai yayi sata da biro ko kuma yayi fashi da makami don sumun kudin da zai je mazabar shi. Idan ba ya so yayi sata, zai fiye mishi ya daina zuwa gabaki daya," dan majalisar Gombe ya kara.

Haka zalika, dan majalisar Kwamoti Laori, wanda ke wakiltar mazabar Numan/Demsa/ Lamurde na jihar Adamawa, ya yi kira ga 'yan majalisa da su wayar da kan mutane game da ayyukan 'yan majalisa a siyasa.

"Yana da matukar wahala ka ga mutane na kawo matsalar mazaba, idan ba matsalar kawunan su ba. Cikin mutane goma, tara daga cikin su na kawo matsalar su ne, saboda haka ba a zabe mu don magance wa wani matsalar shi shi daya ba.

Kara karanta wannan

An kuma: Yaran marigayi Gana sun halaka mai karbar haraji da wasu mutum 3 a Benue

"Naso a ce mutane za su samu ilimi fiye da haka, saboda su iya fuskantar mu; me ku ka yi, me ku ka yanke shawara a kan wannan, me yasa ba ku dawo don samun abubuwa daga garemu ba. Na yaba da hakan, saboda wata dama ce da mutane za su san abubuwan da muke yi, da abunda ya kamata a yi," a cewarsa.
Laori ya kara da fadin, "Da ilimi a kan siyasa za a iya gyara wannan, mutane da dama yanzu sun yi imani da cewa, idan 'yan siyasa suka raba sulalla ne suke aikin da ya dace. Samun ilimin ne zai taimaka wurin gyara hakan."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng