Yanzu-Yanzu: Abokan harkallar Abba Kyari 2 sun amsa laifin da ake tuhumarsu dashi

Yanzu-Yanzu: Abokan harkallar Abba Kyari 2 sun amsa laifin da ake tuhumarsu dashi

  • A yau ne aka gurfanar da Abba Kyari a gaban kotu kan zargin da ake masa na harkallar miyagun kwayoyi
  • Abba Kyari da wasu mutum hudu sun musanta zargin da ake musu, amma an samu wasu biyu da suka amsa laifinsu
  • Ana ci gaba da sauraran halin da za a ji daga kotu, inda a halin yanzu dai ake ci gaba da shari'ar a Abuja

FCT, Abuja - A yau ne aka gurfanar da Abba Kyari da mutum shida da ake zarginsu a wata harkallar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

Bayan kawo Abba Kyari da abokan harkallarsa shida gaban kotu da safiyar yau Litinin, an bijiro da tuhume-tuhume da ake yi musu, sai dai, Abba Kyari da wasu mutum hudu da ake zargi sun musanta zargin da ake musu.

Kara karanta wannan

Don Allah kada ku kai mu magarkama: Abba Kyari da 'yan tawagarsa sun roki kotu

Abba Kyari: Wasu sun amsa laifinsu a shari'at Abba Kyari
Yanzu-Yanzu: Abokan harkallar Abba Kyari 2 sun amsa laifin safarar miyagun kwayoyi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A gefe guda, wasu biyu daga ciki sun amsa laifinsu, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito cewa:

"Yayin da Kyari, sanye da shudin riga, da ‘yan sandan da ake tuhuma tare dashi, suka ki amsa laifin da ake tuhumar su da shi, wadanda ake tuhuma na 6 da na 7, Umeibe da Ezenwanne, sun amsa laifin da aka karanta musu a gaban kotun mai shari’a Emeka Nwite."

Da yake tabbatar da laifin da ya aikata, Umeibe ya kuma roki mai shari'a da ya tausaya masa, inji jaridar The Nation.

DCP Abba Kyari da mutum 6 sun bayyana a kotu, za a gurfanar da su

A wani labarin, Abba Kyari da wasu mutane shida da ake zargi da hannu wajen badakalar miyagun kwayoyi sun bayyana a harabar babban kotun tarayya a Abuja.

Kara karanta wannan

Labari da dumi-dumi: DCP Abba Kyari da mutum 6 sun bayyana a kotu, za a gurfanar da su

The Nation ta kawo rahoto a safiyar Litinin, 7 ga watan Maris 2022 cewa DCP Abba Kyari sun shigo kotu, ana sauraron a gurfanar da su a gaban Alkali.

Jami’an hukumar NDLEA mai yaki da masu safarar miyagun kwayoyi ne suka kai Kyari da ragowar ‘yan sanda da mutane biyu da ake zargi zuwa kotu.

Dakarun NDLEA biyu da suka jagoranci wadannan mutane da ake tuhuma, su na dauke da makamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.