NNPC sun fitar da lita miliyan 380 a kwana 7 domin a kawo karshen wahalar man fetur
- A makon karshe na watan Fubrairu, NNPC sun ce sun fitar da litoci fiye da miliyan 380 na man fetur
- Kamfanin NNPC yana rabawa masu gidajen mai litocin fetur domin a daina wahalar samun mai
- Har yanzu kafin mutum ya sha mai a mafi yawan garuruwan Najeriya, sai ya sha matukar wahala
Abuja - Duk da ikirarin da NNPC ya ke yi na cewa tana fitar da miliyoyin litocin man fetur, har yanzu ana fama da matsanancin wahalar mai a kasar nan.
Wani rahoto da jaridar Punch ta fitar a ranar Litinin, 7 ga watan Maris 2022, ya bayyana cewa NNPC sun saki karin wasu litoci miliyan 381.88 na fetur.
A rahotonsu na mako-mako, kamfanin na NNPC sun ce sun fitar da wadannan miliyoyin litoci a Najeriya ne daga ranar 21 zuwa 26 ga watan Fubrairu 2022.
Hakan na nufin kullum ana raba abin da ya kai lita miliyan 63.65 a tsakanin wannan lokaci. Jimillar alkaluman sun nuna ana cin litoci miliyan 60.86 duk rana.
Kafin wannan makon, NNPC sun yi ikirarin raba litoci miliyan 387.59 daga ranar 14 zuwa 20 ga watan Fubrairu 2022 domin takaita wahalar man da ake yi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda ake yin rabon
Ana raba litocin man fetur din ne daga manyan tashoshin adana mai da ake da su a fadin kasar nan. Reuben Abati sun tabbatar da wannan labari dazun nan.
Kamfanonin da suka fi samun kason na fetur sun hada da Pinnacle-Lekki (lita miliyan 43.25); Aiteo (lita miliyan 22.462); sai A.A. Rano (lita miliyan 22.43).
Akwai A.Y.M Shafa (lita miliyan 19.232) da irinsu kamfanin Prudent da aka ba lita miliyan 17.788.
Rashin mai da rashin wuta: Ku cigaba da juriya, ai ba mulkin Buhari aka fara rashin ba: Femi Adesina
Sauran kamfanonin da NNPC ta ba mai su ne: Gonzaga, Bovas Bulk-Ibafon, PPMC Mosimi, da First Royal. Kamfanonin hudu sun raba kusan lita miliyan 28.
Har gobe akwai layin mai
Duk da wannan kokari da NNPC ke yi, har yanzu ana cigaba da wahalar shan mai. Sai dai rahoton ya ce an samu raguwar dogayen layin motoci a gidajen mai.
Har a babban birnin tarayya na Abuja, ana fama da wahalar man fetur. Mutane su na fitowa shafukan sada zumunta suna bayanin irin azabar da suke sha.
Za a dade ana wahalar mai?
Kwanakin baya aka ji cewa akwai yuwuwar yakin da ake fafatawa tsakanin Russia da Ukraine zai tsawaita karancin man fetur din da ake fuskanta a yau.
Alamu sun nuna yawancin kayayyakin da matata ke samarwa da ake shigowa dasu cikin Najeriya, daga sasannin da ake yakin zasu fuskanci jinkiri.
Asali: Legit.ng