Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri

Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri

  • Kazamar gobara ta lamushe kayan rage radadin 'yan gudun hijira da suka kai darajar naira miliyan goma sha takwas
  • Ana alakanta musababbin gobarar da kone ciyayi inda ta lashe wasu azuzuwan dalibai a kwalejin First Ladies da ke Mariri a Kano
  • Sakataren SEMA na jihar Kano ya bayyana cewa tawagar bincike za ta ziyarci makarantar inda za ta duba yawan barnar kafin gwamnati ta kawo dauki

Kano - A ranar Asabar, mummunar gobara ta tashi inda ta kone kadarorin miliyoyin naira a kwalejin First Ladies da ke Mariri a karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano.

Ana amfani da ginin ne a matsayin wurin adana kayayyaki na hukumar taimakon gaggawa, SEMA na jihar Kano, kuma gobarar ta taba wasu sassan makarantar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Matasan APC a arewa za su siyawa Umahi fam din takara

Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri
Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A yayin bada labarin, sakataren SEMA, Dr Saleh Aliyu Jili ya ce kayan rage radadin sun hada da katifu da matasan kai 900, injinan markade, keken dinki, injinan faci, omon wanki da sauransu duk gobarar ta lamushe.

Ya ce kayayyakin da suka kone duk an karbo su ne daga gwamnatin tarayya domin taimakawa 'yan gudun hijira.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kadarorin da suka kone sun kai darajar miliyan goma sha takwas," ya kara da cewa.

Sakataren hukumar yace ofisoshi, azuzuwa, kwanon rufi da bencina duk sun lalace, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce wata tawagar bincike za ta ziyarci makarantar domin duba yawan barnar da aka samu kafin a mika rahoton ga gwamnatin domin taimako.

"Mai girma gwamna ya mayar da hankali wurin inganta ilimi kuma babu shakka zai dauka dukkan matakin da ya dace domin ganin ya taimaki makarantar da lamarin ya shafa," yace.

Kara karanta wannan

Wuta ta lakume kayayyakin sama da miliyan N18m a siton SEMA a jihar Kano

Ya alakanta gobarar da kone ciyayi da ake yi inda yayi kira ga jama'a da su zama masu kiyayewa.

Ya kara kira garesu da su guje wa kone ciyayi da sauran ayyukan da za su iya kawo gobara da miyagun ibtila'i.

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bakin kakakin hulda da jama'arta, Saminu Abdullahi.

Borno: Mummunar gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijira, daruruwa sun rasa matsuguni

A wani labari na daban, wata gagarumar gobara ta tashi a sansanin 'yan gudun hijira da ke Gamboru Ngala a jihar Borno, lamarin da yasa daruruwan 'yan gudun hijiran suka rasa matsuguni.

Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya auku da yammacin Lahadi inda gobarar ta lamushe wurare masu tarin yawa a sansanin.

Wani jami'in hukumar taimakon gaggawa ta jihar, SEMA, da ke Gamboru Ngala, Malam Yusuf Gulumba, ya sanar da Daily Trust cewa an fara binciken abinda ya kawo gobarar.

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: