Gwamna a Arewa Ya Ce an Gano Ɗanyen Man Fetur Fiye Da Ganga Biliyan 6 Jiharsa

Gwamna a Arewa Ya Ce an Gano Ɗanyen Man Fetur Fiye Da Ganga Biliyan 6 Jiharsa

  • Muhammadu Inuwa Yahaya, Gwamnan Jihar Gombe ya ce kamfanin NNPC ya gano danyen man fetur fiye da ganga biliyan 6 a yankin Kolmani da ke kan iyakar Gombe da Bauchi
  • Inuwa Yahaya ya bawa mutanen jiharsa tabbacin cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba sai ya ga cewa an fara hakar man da iskar gas don jiharsa ta amfana
  • Gwamnan ya ce rashin kudi da kuma annobar COVID-19 da ta janyo tsaiko a kasar ce ta sa aka jinkirta fara hako danyen man da iskar gas amma zai cigaba da bibiyan batun

Gombe - Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce Kamfanin Man Fetur na NNPC ta hannun wata kamfani mai neman man fetur ya gano danyen man fetur fiye da ganga biliyan 6 a yankin Kolmani.

Kara karanta wannan

Bello ya zama Shugaban APC na rikon kwarya, Buhari ya yarda a tuntuke Mala Buni

Ya bada tabbacin cewa gwamntinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin ganin an fara hako man danyen man da aka gano a masarautar Pindiga ta Jihar Gombe, rahoton Nigerian Tribune.

Gwamna a Arewa Ya Ce an Gano Ɗanyen Man Fetur Fiye Da Ganga Biliyan 6 Jiharsa
Gwamnan Gombe Ya Ce an Gano Ɗanyen Man Fetur Fiye Da Ganga Biliyan 6 Jiharsa. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Twitter

Inuwa ya bayyana hakan ne yayin wata liyafa da aka shirya domin karrama alkalin alkalai na wucin gadi na jihar Gombe, Hon Justice Muazu Abdulkadir Pindiga da aka yi a Pindiga a karamar hukumar Akko a ranar Asabar.

Ya ce sau da yawa ya kai ziyara hedkwatan hukumar NNPC kuma ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari don ganin yadda jiharsa za ta fara amfana da man fetur da iskar gas da ke jihar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rashin kudi a kasa da COVID-19 suka janyo jinkirin fara hakar mai a Kolmani, Gwamna Yahaya

Gwamnan ya ce ba domin annobar COVID-19 ba da matsin tattalin arziki da aka shiga a baya-bayan nan, Gwamnatin Tarayya ta kammala shirin fara hako fiye da ganga biliyan 6 na danyen mai a yankin, amma ya bada tabbacin zai cigaba da bada himman ganin an cimma hakan.

Kara karanta wannan

Shugaban Yan Bindiga, Turji: Gwamnati Ba Za Ta Iya Hana Mu Samun Bindiga Ba, Balantana Man Fetur

Babban bako a taron kuma tsohon ministan sufuri, Abdullahi Idris ya yi wa gwamnan godiya bisa jajircewa don ganin an mayar da hankali wurin nemo danyen mai a Kolmani masarautar Pindiga, Nigerian Tribune ta rahoto.

Jihar Gombe da Bauchi ba za su yi rikici a kan Kolmani ba, Sarkin Pindiga

Sarkin Pindiga, Muhammad Seyoji Ahmed, a jawabinsa ya ce abin da ke kama da rashin jituwa tsakanin Jihohin Gombe da Bauchi kan filin hako danyen man na Kolmani ba zai janyo rikici tsakanin jihohin ba.

2023: Manya masu son satar dukiyar talakawa ne ba su son a sake samun wani Buharin, Garba Shehu

A wani labarin daban, Fadar Shugaban Kasa ta ce manyan mutane masu aikata rashawa ne ba su son a sake samun 'wani Buhari' a Najeriya saboda wata manufarsu na gina kansu, Daily Trust ta ruwaito.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce zai yi wahala a samu wani shugaba da zai iya zarce irin ayyukan da Buhari ya yi.

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

Ya yi bayanin kan dalilin da yasa Buhari ba zai 'bari a cigaba da yadda ake harka' a kasar ba a karkashin gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164