Sanatan Amurka Ya Buƙaci a Yi Wa Putin Kisar Gilla, Rasha Ta Yi Martani
- Lindsey Graham, Sanata dan jam'iyyar Republican mai wakiltan South Carolina ya bukaci wani daga cikin na hannun daman Putin ya halaka shi
- Graham ya ce halaka Shugaban Rasha Vladimir Putin ne kadai hanya daya da za a kawo karshen yakin da Rasha ta afkwa Ukraine
- Anatoly Antonov, jakadan kasar Rasha a Amurka ya yi tir da kalaman na Graham yana mai cewa wuce gona da iri ne kuma ba za a amince da shi ba
Sanata a Amurka ya yi kira ga wani daga cikin na hannun daman Shugaba Vladimir Putin ya yi masa kisar gilla.
Lindsey Graham ya ce hanya daya tilo da za a kawo karshen kutsen da Rasha ke yi Ukraine shine 'wani a Rasha ya kawar da wannan mutumin,' rahoton BBC News.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a Twitter, Sanatan dan jam'iyyar Republican ya yi tambayi idan akwai 'Brutus' da zai iya kawar da Mr Putin ya kawo karshen yakin.
Mr Graham, wanda ke wakiltan South Carolina, ya wallafa a Twitter:
"Za ka yi wa kasarka da duniya gagarumin aiki.
"Shin akwai Brutus a Rasha? Akwai wanda ya fi Kwanel Stauffenberg nasara a sojojin Rasha?"
Shin wanene Brutus?
Brutus dan siyasa ne a dan kasar Rome wanda ya yi wa Julius Caesar, kisar gilla, yayin da Sojan Jamus, Kwanel Claus Stauffenberg ya yi suna ne saboda yunkurin kashe Adolf Hitler a 1944.
Kalamansa ya fusata Jakadan Rasha a Amurka
Anatoly Antonov, jakadan Rasha a Amurka ya bayyana kalaman na Graham a matsayin 'wuce gona da iri kuma abin da ba za a amince da shi ba.'
'Karin Bayani: Zan Sayar Da Chelsea, Zan Ba Wa Mutanen Da Yaƙi Ya Ritsa Da Su A Ukraine Kuɗin, Abramovich
Ya ce irin kiyayya da kyama da ake yi wa Rasha a Amurka ya wuce misali.
"Abin mamaki ne sanatan kasar da ke koyar da halayen da'a ga sauran duniya zai iya kira ga cewa a aikata ta'addanci domin cimma burin Washington 'Amurka' a idon kasashen duniya."
Amurka ta nesanta kanta daga kalaman Sanata Graham
A ranar Juma'a, sakataren White House Jen Psaki ya bayyana cewa kalaman Mr Graham ba shine matsayar gwamnatin Amurka ba kuma ba kalamai bane da za ji daga bakin wani da ke yi wa gwamnati aiki.
Asali: Legit.ng