Mafi girma a Turai: Bayanai 6 game da tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia da Putin ya lalata a Ukraine

Mafi girma a Turai: Bayanai 6 game da tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia da Putin ya lalata a Ukraine

  • Ana ci gaba da yaki tsakanin Ukraine da Rasha, lamurra na kara baci a wasu yankunan kasar Ukraine
  • Rasha na ci gaba da harba makamai kan kasar Ukraine, lamarin da ke kara jawo cece-kuce a kasashen duniya
  • A makon nan ne kasar Rasha ta lalata wata tashar makamashin nukiliya, mun kawo muku bayanai a kanta

Ukraine - Jaridar Guardian ta ruwaito cewa, da sanyin safiyar Juma'a 4 ga watan Maris ne wuta ta kama tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia dake Enerhodar na kasar Ukraine, bayan da sojojin Rasha suka yi luguden wuta a wurin.

Yayin da ake ci gaba da kashe wutar, hukumomin Ukraine sun ce dakarun Rasha sun kwace ikon tashar makamashin ta nukiliya, kamar yadda Al Jazeera ta ruwaito.

Yadda aka lalata tashar makamashin nukiliyar da aka lalata a Ukraine
Mafi girma a Turai, wasu bayanai game da tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia da Putin ya lalata | Hoto: sawahpress.com
Asali: UGC

To amma, wane muhimmanci wannan tashar take dashi haka da ta dauki hankalin shugaba Vladimir Putin na Rasha?

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

Bayanai game da Zaporizhzhia

Ga wasu bayanai game da tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia.

  1. An gina tashar makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia tsakanin 1984 zuwa 1995.
  2. Ita ce tashar nukiliya mafi girma a nahiyar Turai kuma ta tara mafi girma a duniya.
  3. Cibiyar mai samar da wutar lantarki tana Kudu maso Gabashin Ukraine ne a cikin birnin Enerhodar a gabar tafkin Kakhovka a kan kogin Dnieper.
  4. Tashar makamashin Nukiliya ta Zaporizhzhia tana da bangarorin samar da wuta guda shida, kowacce tana samar da megawat 950 na wutar lantarki, megawat 5,700 a jumilance.
  5. Makamashin da tashar makamashin nukiliyar ke samarwa ya isa ya ba da wutar lantarki ga kusan gidaje miliyan 4.
  6. A karkashin yanayi na yau da kullum, tashar na samar da kashi daya cikin biyar na wutar lantarkin Ukraine da kusan rabin makamashin da cibiyoyin makamashin nukiliya na kasar ke samarwa.

Kara karanta wannan

Mun shirya: Najeriya za ta fara gina tashar makamashin nukiliya, ta hada kai da Rasha, da wasu kasashe

N56,000 za mu baku: FG za ta raba wa wadanda suka dawo daga Ukraine kudin kashewa

A wani labarin, shugabar hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta ce karin jirage guda biyu da ke kwashe ‘yan Najeriya daga kasar Ukraine za su iso a yau dinnan.

Kashi na farko na 'yan Najeriya da suka tsere daga mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine sun iso Abuja da safiyar yau Juma'a.

‘Yan Najeriya 411 da suka hada da dalibai da ma’aikatan ofishin jakadanci sun isa filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikwe da ke Abuja da safiyar yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.