Dalilin da yasa aka jinkirta jigilar yan Najeriya da yaki ya ritsa da su a Ukraine ranar Alhamis

Dalilin da yasa aka jinkirta jigilar yan Najeriya da yaki ya ritsa da su a Ukraine ranar Alhamis

  • Yayinda jirgi ya shirya jigilar wadanda yaki ya ritsa dasu, mafi akasarin yan Najeriya sun ce ba zasu hau ba
  • Wannan shine dalilin da ya sabbaba dage jigilar da aka shirya yi ranar Laraba da Alhamis, wani babban jami'i ya bayyana
  • Tuni dai kun ji cewa yan Najeriya mazauna Ukraine da dama sun ce gwanda su mutu a can da su dawo gida

Abuja - Dalilin da ya sa gwamnatin tarayya ta jinkirta jigilar yan Najeriya mazauna Ukraine zuwa gida ranar Alhamis kamar yadda akayi alkawari ya bayyana.

Daily Trust ta ruwaito wani babban jami'in gwamnati da cewa wasu cikin wadanda ake kokarin jigila sun ki hawa jirgi saboda basu son dawowa Najeriya.

Tun lokacin da yakin ya barke, wasu sun gudu Romania, Hungary, Slovakia da Poland don neman mafaka.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Jirgin jigilar yan Najeriya mazauna Ukraine na biyu ya dira birnin tarayya Abuja

An shirya fara jigilarsu ranar Laraba kuma jiragen MaxAir da Air Peace sun dira Turai don kwasansu amma aka dage jigilar ba tare da bada wani dalili ba.

Yayinda yan jaridar da suka dira tashar jirgin Nnamdi Azikwe don tarbarsu suka tambayi dalili, an ce wasu matsala aka samu.

Dalibai
Dalilin da yasa aka jinkirta jigilar yan Najeriya da yaki ya ritsa da su a Ukraine ranar Alhamis Hoto: Dalibai
Asali: UGC

Amma wani babban jami'n gwamnati wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya bayyana cewa an dage jigilar ne saboda yan Najeriyan basu son dawowa.

A cewarsa:

"Rashin son hawa jirgi ya sa aka gaza jigilar. Wadanda suka yarda su dawo basu wuce rabin adadin cika jirgi ba. Kuma kamfanonin jiragen sun ce ba zasu tashi da rabin fasinja ba."
"Amma dai an daidaita lamarin yanzu, wasu sun yarda daga baya su dawo. Nan da ranar Juma'a zasu dawo."

Kara karanta wannan

Wahalar Mai: Annaru ta ci dan bunburutu da matarsa da sukayi ajiyan jarkokin mai a gida

Wasu yan Najeriyan da muke kokarin kwasowa daga Ukraine sun ce ba zasu dawo ba, Minista waje

A bayanmun kawo muku labarin cewa wasu yan Najeriyan da suka makale a Ukraine sakamakon yakin kasar da kasar Rasha basu da niyyar dawowa gida.

Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyema, ya bayyana hakan lokacin da ya gana da Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ranar Litinin.

Gwanda mu mutu da mu koma Najeriya, Wasu yan Najeriyan dake kasar Ukraniya

Wasu yan Najeriya dake zaune kasar Ukraniya yanzu haka sun yi watsi da maganar gwamnatin tarayya na kwasosu daga can sakamakon yakin kasar da Rasha

Daily Trust ta ruwaito wasu yan Najeriya na cewa sun gwammace yaki ta ci su da su dawo gida Najeriya.

Treasure Chinenye Bellgam, wani dalibi ya ce abinda gwamnatin Najeriya ke kokarin yi na da kyau amma,

"Mafi akasarin yan Najeriya kudi suka zo nema kuma ba zasu yarda su koma Najeriya ba, sun gwammace su mutu a nan."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng