AbdulJabbar ya gabatar da litattafai 27 a kotu, ya rantse da Al-Qur'ani bai zagi Annabi ba
- An cigaba da zaman kotu kan shari'ar dake gudana tsakanin Malam AbdulJabbar da Gwamnatin Kano
- A yau AbdulJabbar ya fara gabatar da nasa hujjojin kan kalaman da ake zarginsa da yi
- Alkalin kotun ya dage karar zuwa ranar 17 ga Marus don cigaba da zaman
Kano - A ranar Alhamis, Sheikh Abduljabbar Nasiru-Kabara, ya fara gabatar da nasa hujjojin gaban kotu a shari'ar dake gudana tsakaninsa da gwamnatin jihar Kano.
AbdulJabbar ya gabatar da litattafai 27, ciki akwai Almuhadisu Alfasil Banul Rawawil Wali, Sunannun Darumi, Jami’u Ilmi, Tauhiful Afkar, Anannakatu Almukaddimatu Ibn Salah, Al Gaya, dss.
A baya mun ruwaito cewa an shigar da Malam AbdulJabbar kotu bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Gabanin fara jawabinsa yau a kotu, AbdulJabbar ya rantse da Alqur'ani mai girma cewa bai zagi Annabi ba, rahoton NAN.
Yace:
"Kawai ina kare mutuncin Annabi Muhammad (SAW) ne bisa kalaman da akayi akansa a cikin Hadisi."
"Abinda na gani cikin Hadisi na fassara. Ban sharhin kaina bane."
"A wa'azuzzuka na, ban yi batanci wa Annabi ba kan aurensa na Nana Safiya."
Lauyan gwamnati, Suraj Sa'eda SAN ya bayyanawa kotu cewa AbdulJabbar ya yi kalaman batanci wa Annabi kan aurensa da Nana Safiyya a Jautul Fara a sashe na 93 (40) da hadisi da 1,365 da 1,428.
Alkalin kotun, Malam Ibrahim Sarki-Yola, ya bukaci AbdulJabbar ya baiwa lauyan gwamnati kwafin litattafan.
Ya dage karar zuwa ranar 17 ga Marus don cigaba da zaman.
Asali: Legit.ng