An kuma: Yaran marigayi Gana sun halaka mai karbar haraji da wasu mutum 3 a Benue
- 'Yan bindiga da ake zargin yaran marigayi Terwase Akwaza wanda aka fi sani da Gana sun halaka mai karbar haraji a Benue
- Kamar yadda mazauna yankin suka sanar, sun halaka wasu mutum ukun a kuayen Kundi na gundumar Mbache da ke Katsina-Ala
- Wannan mummunan al'aamari yanaa zuwa ne bayan kwanaa kacal da 'yan bindiga suka kai makamancin farmaki inda suka kashe sarki da 'yan zaman makoki
Benue - An sake samun labarin yadda 'yan bindiga da ake zargin magoya bayan marigayi Terwase Akwaza, wanda ake wa lakabi da Gana ne suka halaka wani mai amsar haraji da wasu mutane uku a kauyen Imande Kundi a gundumar Mbache na karamar hukumar Katsina-Ala dake jihar Biniwe.
Al'amarin ya auku ne bayan kwana hudu kacal da 'yan bindigan suka kai wa wani yankin dake makwabtaka kwatankwacin harin a cikin gunduma daya, wanda yayi sanadiyyar lashe rayukan sarkin kauyen da masu zaman makoki guda takwas.
Wata majiya a yankin ta bayyana wa Vanguard yadda 'yan bindiga suka auka yankin a ranar Laraba misalin karfe 3:00 na rana, inda suka budewa mutane wuta.
"Hudu daga cikin mutanen sun rasa rayukansu, yayin da wasu suka samu raunuka. A halin yanzu da muke maganar, mutane suna ta hijira daga yankin. Ana zargin 'yan bindigan da zama yaran marigayi Gana.
"Lamarin nan ya auku a wannan dai gundumar Mbacher, inda aka halaka sarkin yankin tare da 'yan zaman makoki guda takwas, wasu kwanaki da suka wuce," a cewarsa.
Yayin tabbatar da aukuwar lamarin, Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Mr Alfred Atera ya bayyana yadda aka shaida wa kwamandan 'yan sandan yankin da DPO anguwan aukuwar lamarin.
Atera ya ce, "Da gaske ne wasu 'yan ta'adda sun kai farmaki a wannan dai yankin, misalin karfe 2:30 zuwa 3:00 na rana, inda suka aukawa 'yan zaman makoki a ranar Asabar, a wannan lokacin sun halaka mutane hudu.
"Daya daga cikin mutanen da suka halaka shine, mai amsar haraji, sannan na kai korafi game da lamarin ga kwamandan 'yan sanda na yankin da DPO na Katsina Ala."
An yi iya kokarin tuntubar kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Catherine Anene, amma hakan bai yuwu ba.
Ortom ga FG: Ku ayyana Miyetti Allah a matsayin kungiyar ta'addanci
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya ayyana kungiyar makiyayan shanu ta Miyetti Allah, MACBAN, a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.
Kiran ya biyo bayan yadda gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, TheCable ta ruwaito.
A wata takarda wacce sakataren watsa labaran gwamnan, Nathaniel Ikyur ya saki, ya yanko inda gwamnan ya ce kungiyar tana kawo tashin hankali a Binuwai.
Asali: Legit.ng