Ana kokarin biyawa ASUU bukatunta, Minista ya fadi kudin da aka ba Malaman jami’a
- Ministan kwadago na tarayya, Chris Ngige ya zauna da Muhammadu Buhari kan yajin-aikin ASUU
- Dr. Chris Ngige ya ce daga karshen 2020 zuwa yanzu, gwamnati ta biya ‘Yan ASUU fiye da N90bn
- Shugaban ASUU ya ce sun gaji da sa hannu a takardu, su na sauraron gwamnati ta cika alkawura
Abuja - Ministan kwadago na kasa, Chris Ngige ya ce gwamnatin tarayya na kokari wajen ganin ta shawo kan sabaninta da kungiyar malaman jami’a.
The Cable ta ce Dr. Chris Ngige ya zanta da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa a ranar Talata bayan ya hadu da Muhammadu Buhari a kan batun yajin-aikin.
Ministan ya bayyana cewa daga Disamban 2020 da aka sasanta da kungiyar ASUU, gwamnatin tarayya ta biya malaman jami’a fiye da Naira biliyan 92.
Chris Ngige ya shaidawa 'yan jarida cewa gwamnatin Buhari ta cika alkawarin da ta yi na biyan alawus din karin aiki na 2020, an saki Naira biliyan 40.
Baya ga EAA, an ware Naira biliyan 30 domin gyaran jami’o’i, kuma an biya kudin a shekarar bara.
Ngige ya ce an amince a biya malaman kudin alawus din 2021 daga sabon kasafin da aka turawa majalisa, a nan ma gwamnati ta biya Naira biliyan 22.127.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rikicin IPPIS
Haka zalika Ministan kwadagon ya bada tabbacin cewa su na la’akari da korafin da kungiyar ASUU take yi a kan manhajar IPPIS da ake biyan albashi.
Malaman jami’o’i suna so ne a rika biyan su albashinsu da manhajar UTAS da suka kirkiro. Ministan ya ce NITDA ta gano kura-kurai tattare da UTAS.
Sai dai ‘yan ASUU sun sake aikawa hukumar NITDA takarda, su na cewa binciken na ta ba daidai ba ne. Zuwa yanzu gwamnati ba ta karbi bukatar kungiyar ba.
Mun gaji da gafara sa! - ASUU
Jaridar Premium Times ta rahoto shugaban ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke yana cewa sun gaji da sa hannu a yarjejeniyar MoU da gwamnati.
Emmanuel Osodeke ya ce abin da kurum suke bukata a yanzu shi ne a cika alkawuran da aka yi masu. Farfesan ya ce biya masu bukatunsu ba zai ci lokaci ba.
Za a rufe sauran makarantu?
A makonnin da suka wuce ne aka samu rahoto cewa kungiyar COEASU ta fara nuna alamun za a tafi yajin aiki a makarantun FCE idan har gwamnati ta yi wasa.
Shugaban kungiyar COEASU na kasa baki daya, Dr. Smart Olugbeko ya ce an dauki lokaci gwamnatin tarayya ta na raina musu hankali a kan hakkokinsu.
Asali: Legit.ng