Ko hannun Tinubu na rawa haka zamu zabeshi shugaban kasa a 2023, Jibrin
- Tsohon dan majalisar wakilan tarayya, AbdulMumini Jibrin ya yi martani kan bidiyon dake yawo a kafafen sada zumunta
- A karshen makon da ya gabata, Tinubu ya bayyana cewa shi matashi ne kamar sauran matasa
- A yayin da yake magana, wasu sun bayyana cewa hannunsa na rawa wanda ke nuna bai da cikakken lafiya
Abdulmumin Jibrin, Dirakta Janar na majalisar kungiyoyin magoya bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa jigon APCn ne mutum daya tilo da zai iya kada kowa a zaben shugabancin kasar 2023.
Jibrin ya bayyana hakan ne yayin martan kan takarar Tinubu a 2023.
Hotuna da bidiyoyi sun nuna hannun Bola Tinubu sun rawa lokacin da yake jawabi karshen makon da ya gabata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Martani kan hakan a shafinsa na Tuwita. Jibrin yace:
"Ko hannunsa na rawa, shine zabinmu. Baku isa ku hanamu demokradiyya ba. Ku je ku nemi naku yan takaran da hannunsu basu rawa."
"Mu hadu a ranar zabe. Duk inda Asiwaju yayi, nan muka yi."
"Dole dama a samu wasu yan tsiraru suna yada sakonnin adawa. Kamar kowani shugaban kasa, ba za'a daina sukarsu ba lokacin zabe da kuma lokacin mulkin Tinubu."
Siyasar 2023 ta matasa ce: Ni fa ba tsoho bane, ni matashi ne mai jini a jika, inji Tinubu
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana kansa a matsayin matashi.
Tinubu ya yi furucin ne a daidai lokacin da ake kiraye-kirayen a baiwa matasa damar yin mulki
Da yake tabbatar da cewar yana da karfin jagorantar kasar, Tinubu ya ce yana da ikon yi wa Najeriya hidima da kuma daukaka kasar.
Ya fada ma magoya bayansa a wani taro da aka yi kwanan nan cewa APC za ta ci gaba da kare ra’ayin yan Najeriya a gida da waje.
“Gani a nan tsaye a gabanku…kuma ni matashi ne,” cewar Tinubu yayin da magoya bayansa ke kara masa karfin gwiwa.
Asali: Legit.ng