Budurwa ta gwangwaje matashi dake doguwar tafiya zuwa makatanta da dalleliyar mota
- Wata mata mai matukar kirki, mai suna Lavonda Wright Myer, ta jefa wani dalibin makarantar sakandare dake takawa da kafarsa na tsawon awanni kafin ya isa wurin aiki, cikin farinciki
- A ranar da ta fara haduwa da matashin dan shekara 18, mai suna Jayden Sutton, Myers ta daukar wa kanta alkawarin siya masa sabuwar mota, sannan tayi nasarar cikawa
- Yayin bayyana abunda ya bata kwarin gwuiwar yin hakan, 'yar kasuwar ta ce, zuciyar shi da jajircewa ne yasa ta zubda hawaye
Jajircewa da neman na kan wani yaro, ya janyo masa kyauta daga wacce bai sani ba da tayi sanadiyyar canza rayuwarshi gaba daya.
Wani yaro dalibin makarantar sakandare dan shekara 18, mai suna Jayden Sutton daga yankin Cobb na Georgia dake Turai, ya sha matukar mamaki yayin da wata mata mai matukar kirkin wacce ta rage mishi hanya a motar ta, ta yi masa gagarumar kyauta.
Becauseofthemwecan ta ruwaito yadda Jayden ke aiki a wurin cin abinci bayan tashi daga makaranta don kawai ya tara kudin cika burin sa na siyan mota.
Saboda tsabar jajircewa matashin mai karancin shekaru na takawa da kafarsa kimanin mil bakwai, bayan tashi daga makaranta karfe 3:30 na rana don daukar awa 6 zuwa 7 a gurin siyar da abinci.
A lokacin da ya gama aikin Jayden yana sake takawa da kafarsa har ya isa gida wurin karfe 11:30 na dare.
A wata rana mai cike da abubuwan ban al'ajabi, 10 ga watan Disamba, 2020, wata mata mai suna Lavonda Wright Myers na tuki a motar ta yayin da ta hangi yaron yana tafiya cikin ruwan sama.
A lokacin da 'yar kasuwar ta rage mishi hanya, sai ta fahimci dalilin da yasa yake tafiya mai nisa a kasa, saboda ba shi da arzikin hawa motar haya.
Kotu ta tsinke aure bayan mata ta kama mijinta turmi da tabarya da wata kuma ya zaneta saboda ta koka
"A lokacin da na aje shi wurin aikin, zuciyarsa da jajircewarsa ce ta sa ni zubda hawaye. Ya ce ranki shi dade, ina aiki ne, saboda ya zame min dole.
"Ya yi murmushi cikin farinciki, kuma wannan yaron ya cancanci a saka mishi albarka," ta bayyana wa manema labarai.
Daga lokacin ne ta lashi takobin gwangwaje shi da zukekiyar mota, kana ta wallafa labarin sa a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, gami da bude mishi shafin GoFundme. Wanda cikin kwanaki da budewa, ya sami tallafin $6,635 (N7 miliyan).
Tayi ciniki da mai siyar da mota da ya rage mata farashin mota kirar Honda ta $7,800(N3.2 miliyan) zuwa $7,000(2.9 miliyan), sannan ta cikasa $635 daga kudin ta.
Jayden ya shiga cikin matukar farin ciki tare da nuna godiya mai dumbin yawa ga Myers bisa kyautar da tayi masa.
Ya ce a kalaman shi:
"Ina kaunar ta saboda haka. Kawai ina so in miki godiya mai yawa, ba za ki gane yawan godiyar da nake miki ba.
"Na san da cewa koda nayi aiki kullum saboda in siya mota, zan iya siya. Idan kana wani abu mai kyau, ko kokarin cimma manufa, ka cigaba da yin hakan. Za ka iya samun taimako. Hakan ya faru a kaina."
Asali: Legit.ng