Jerin gyaran fuska 8 da aka yiwa kundin tsarin mulkin Najeriya yau a majalisa
Majalisar dokokin tarayya wacce ta hada majalisar dattawa da majalisar wakilai sun fara kada kuri'a kan sauye-sauye 68 na cigaba da aka gabatar game da garambawul na kundin tsarin mulkin kasa.
A ranar Talata, yan majalisun biyu sun yanke shawara kan wasu ciki.
Yayinda suka amince da wasu gyara-gyaren, sun yi watsi da wasu.
Legit ta tattaro muku jerin abubuwan da yan majalisan suka yi zabe kai a yau:
1. Majalisa ta amince da kudurin takara ga 'yan takara masu zaman kansu
Majalisar dattijai ta amince da kudirin doka mai lamba 58 da ke neman bai wa ‘yan takara masu zaman kansu damar tsayawa takara.
Kudurin zai shafi ‘yan takarar shugaban kasa, na gwamna, da ‘yan majalisun tarayya, da na majalisun jihohi, da na kananan hukumomi.
2. Majalisa ta yi watsi da kudirin baiwa yan Najeriya mazauna kasashen waje damar kada kuri'a a zabe
Majalisar dattawa ta yi waje da bukatar baiwa yan Najeriya mazauna kasashen waje damar mushakara a zabukan dake gudana a nan gida.
3. Majalisa ta yi watsi da kudirin baiwa birnin tarayya Abuja Magajin Gari
Majalisa ta ki amincewa da kudirin samar da sabon kujeran magajin gari ga birnin tarayya Abuja.
4. Wajabta nadin dan asalin Abuja matsayin Ministan Abuja
Majalisa ta yi waje da kudirin wajabtawa Shugaban kasa nada dan asalin birnin tarayya Abuja matsayin Ministan garin.
5. Kudirin wajabta ilmi kyauta
Majalisa ta amince da kudirin wajabtawa yara samun ilimi kyauta. Hakazalika ilmi ya zama hakki na dukkan dan Najeriya.
6. Majalisa ta amince da dokar tsare arzikin abinci
7. Majalisar tarayya ta kaɗa kuri'ar kin amincewa da kudirin kirkiro wa mata kujeru na musamman
Majalisun dokokin sun yi watsi da dokar samawa mata kujeru akalla 10 a matsayin kwamishanoni a jiha kuma akalla 10 matsayin Ministoci.
Majalisar dattawan ta kaɗa kuri'ar rashin amincewa da dokar kirkiro wa mata kujeru na musamman majalisun tarayya da jihohi. Kudirin dokar ya samu koma baya yayin da Sanatoci 30 suka amince, kuma mutum 58 suka kaɗa kuri'ar kin amincewa.
8. Yan Majalisar Wakilai Sun Ki Amincewa da Fansho Na Har Abada Ga Shugabannin majalisa
Mambobin majalisar wakilai na tarayya sun ki amincewa da wata yunkuri na yi dokar biyan fansho na har abada ga shugabannin majalisar tarayya.
Kuri'u guda 193 ne aka kada a majalisar wakilan na neman bada fansho na har abada ga shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai da mataimakansu.
Yan majalisa guda 162 sun ce a'a yayin da guda 3 ba su kada kuri'ar ba.
Asali: Legit.ng