Da Duminsa: Majalisun tarayya sun yi watsi da kudurin ware wa mata Kujeru, da kudirin VAT
- Majalisar tarayya ta kaɗa kuri'ar kin amincewa da kudirin kirkiro wa mata kujeru na musamman da kudirin canza wa VAT wuri
- Majalisar wakilan tarayya da kuma majalisar dattawa duk ba su amince da kudirorin ba a zaman garambawul ga kundin mulki 1999
- Majalisun biyu na cigaba da zaman duba abubuwa 68 da aka gabatar game da garambawul na kundin mulkin kasa
Abuja - Majalisar tarayya a Najeriya ta yi fatali da kudirin samar da kujeru na musamman ga mata da kuma na canza wa biyan harajin VAT wuri zuwa jerin Waje.
Daily Trust ta rahoto cewa mambobin majalisar sun yi watsi da kudirorin biyu ne yayin kaɗa kuri'a kan abubuwa 68 da aka maida hankali wurin gyaran kwansutushin, ranar Talata.
Majalisar wakilai ta kasa
A majalisar wakilan tarayya, Mambobi 209 suka kaɗa kuri'ar kin amincewa da canza wa VAT wuri, yayin da mambobi 208 suka ki amincewa da ware wa mata kujeru na musamman.
Kudirin VAT ya ce: "Kudurin doka domin canza sashi na I a garambawul na Kundin Mulkin Najeriya 1999, a sanya tsarin biyan harajin VAT a cikin jerin Exclusive List, da abubuwan da suka shafi haka."
Kudirin kirkiro wa mata kujeru na musamman ya ce: "Kudirin doka domin garambawul ga kundin dokokin mulkin ƙasa 1999 da zai ware wa mata kujeru na musamman a majalisun tarayya da na jihohi, da makamancin haka."
Majalisar dattawa
A majalisar dattawa, Sanatoci 41 suka amince da canza wa VAT wurin zama, yayin da 44 suka ki amincewa, wanda hakan ya gaza kashi 2 cikin 3 na mambobin majalisa.
Hakanan kuma majalisar dattawan ta kaɗa kuri'ar rashin amincewa da dokar kirkiro wa mata kujeru na musamman majalisun tarayya da jihohi.
Kudirin dokar ya samu koma baya yayin da Sanatoci 30 suka amince, kuma mutum 58 suka kaɗa kuri'ar kin amincewa.
Kudurin ya ƙunshi kirkirar kujeru na musamman na mata kaɗai a majalisar dattawa da wakilai da kuma majalisun dokokin jihohi.
A wani labarin na daban kuma Sabon mataimakin gwamna Matawalle ya yi murabus daga kujerar Sanata
Sanata Mai wakiltar jihar Zamfara ta tsakiya, Sanata Hussaini Nasiha, ya yi murabus daga kujerarsa ta majalisa a hukumance.
Jaridar Puch ta rahoto cewa ya ɗauki wannan matakin ne biyo bayan naɗa shi mataimakin gwamna da Gwamna Matawalle ya yi a Zamfara.
Asali: Legit.ng