'Karin Bayani: 'Yan Majalisar Wakilai Sun Ki Amincewa da Fansho Na Har Abada Ga Shugabannin NASS
- Yan majalisar wakilai sun ki amincewa da kudirin dokar biyan shugaban majalisar dattawa da wakilai da mataimakansu fansho na har abada
- Hakan ya faru ne bayan zaman majalisar da aka yi a ranar Talata aka kuma yi kuri'a a majalisar kuma wadanda suka ki amincewa suka yi rinjaye
- Shugaban majalisar dattawa, Sanata Lawan Ahmed ya ce kudirin dokar bata samu karbuwa ba kwata-kwata
Mambobin majalisar wakilai na tarayya sun ki amincewa da wata yunkuri na yi dokar biyan fansho na har abada ga shugabannin majalisar tarayya, rahoton Daily Trust.
Mambobin sun ki amincewa da kudin dokar da ya ce:
"Kudirin doka domin yin garambawul ga kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 domin bada fansho na har abada ga shugabannin majalisar tarayya; da wasu abubuwa da suka shafe hakan da amincewa da su."
Kuri'u guda 193 ne aka kada a majalisar wakilan na neman bada fansho na har abada ga shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai da mataimakansu, rahoton Vanguard.
Yan majalisa guda 162 sun ce a'a yayin da guda 3 ba su kada kuri'ar ba.
A majalisar dattawan, Shugaban Majalisa, Ahmad Lawan ya ce, "Kudirin dokar ba ta samu amincewa ba kwata-kwata."
Majalisun tarayya sun yi watsi da kudurin ware wa mata Kujeru, da kudirin VAT
Majalisar tarayya a Najeriya ta yi fatali da kudirin samar da kujeru na musamman ga mata da kuma na canza wa biyan harajin VAT wuri zuwa jerin Waje.
Daily Trust ta rahoto cewa mambobin majisar sun yi watsi da kudirorin biyu ne yayin kaɗa kuri'a kan abubuwa 68 da aka maida hankali wurin gyaran kwansutushin, ranar Talata.
A majalisar wakilan tarayya, Mambobi 209 suka kaɗa kuri'ar kin amincewa da canza wa VAT wuri, yayin da mambobi 208 suka ki amincewa da ware wa mata kujeru na musamman.
Asali: Legit.ng