Tashin Hankali: An tsinci gawar mai haɗa wa Mataimakin shugaban ƙasa takalmi a daki a Abuja

Tashin Hankali: An tsinci gawar mai haɗa wa Mataimakin shugaban ƙasa takalmi a daki a Abuja

  • Omale Ojima mai haɗa Takalma a babban birnin tarayya Abuja, ya mutu daga kwanciya bacci a ɗakinsa dake Kubwa
  • Wani mazaunin yankin ya ce lokacinsa ne ya yi, domin ya kwanta lafiya lau, da safiyar Lahadi aka tsinci gawarsa a daki
  • Mataimakin shugaban ƙasa, wanda mamacin ya taba haɗa wa takalma ya yi jajen rasuwarsa a wata sanarwa

Abuja - Wani mai haɗa takalma, Omale Ojima, (Ojbest) wanda ya taɓa haɗa wa mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, takalma, ya mutu a ɗakinsa dake Kubwa, Abuja.

Daily Trust ta rahoto cewa an gano gawar mamacin da safiyar Lahadi a yankin Pipeline dake Kubwa, karamar hukumar Bwari, ya bar mazauna yankin cikin kaɗuwa da tashin hankali.

Osinbajo da Ojbest
Tashin Hankali: An tsinci gawar mai haɗa wa Mataimakin shugaban ƙasa takalmi a daki a Abuja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Adeleye Gbenga, dake zaune a yankin da lamarin ya auku, ya ce marigayin ya mutu ne a bacci, kuma an tsinci gawarsa da misalin ƙarfe 6:00 na safe.

Kara karanta wannan

Uwar gida ta danna wa Mijinta wuka har lahira daga zuwa bankwana zai koma dakin Amarya

Gbenga ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na samu labari da karfe 6:00 na safe ranar Lahadi cewa ya kwanta bacci amma bai tashi ba. Tuni aka kai gawarsa dakin gawa na babban Asibitin Kubwa."

Yaushe ya haɗa wa Osinbajo Takalma?

Rahotanni sun nuna cewa Marigayi Ojbest ya shahara ne lokacin da ya yi amfani da #Osinbajo wajen tallata kayansa a Twitter, kuma har ta kai ga ya haɗa wa Osinbajo takalma.

"Ba zan iya rike farin cikin da nake ciki ba, wannan mafarki na ne da ban taɓa tunanin zai zama gaskiya ba. Na rasa kalmar da zan yi amfani da ita, amma ina matukar gode wa Yemi Osinbajo, bisa taimakonsa da goyon bayan Objest Footwear."

- Inji Marigayi Ojima lokacin da ya kaiwa Osinbajo Takalma.

Shin Osinbajo ya samu labarin abin da ya faru?

Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi ta'aziyyar rasuwar mutumin, inda ya bayyana shi da ɗan kasuwan takalma kuma aboki.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani ma'aikacin jami'a ya mutu a cikin ruwan shakatawa a Hotel

A wata sanarwa da ya rattaba wa hannu da kansa, Osinbajo, ya ce bai ji daɗin labarin rasuwar Mr. Ojima Omale ba.

"Ni da yan tawaga ta da ya taba haɗa mana Takalma, za mu yi kewarsa da aikinsa. Kalaman mu na tare da iyalansa, Allah ya ba su hakuri."

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun bindige Hadimin gwamna har Lahira a wurin ta'aziyya

Wani wanda ke tare da mamacin ya bayyana cewa sun baro wurin Jana'izar da suka halarta yayin da maharan suka tare su.

A halin yanzun dakarun sojoji sun bazama cikin daji domin nemo gawar mutumin, bayan sun yi gaba da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262