Uwar gida ta danna wa Mijinta wuka har lahira daga zuwa bankwana zai koma dakin Amarya
- Tsagwaron kishin mata ya yi sanadin rasuwar wani Mai mata biyu yayin da yake yi wa Uwar gida bankwana zai koma dakin Amarya
- Rahoto ya nuna cewa Uwar gidan mai suna Atika ta daba wa mijinsu wuka har lahira a Mararaba dake jihar Nasarawa
- Duk da kokarin cetonsa da Amarya ta yi bayan faruwar lamarin, Likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa a Asibiti
Nasarawa - Wata matar Aure mai suna, Atika, ta daba wa maigidanta wuka har lahira a Mararaba, karamar hukumar Karu, jihar Nasarawa.
Lamarin kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ya auku ne ranar Asabar da daddare yayin da magidancin ya shiga ɗakin matar.
Magidancin mai suna Ibrahim Salihu, ɗan kimanin shekara 37, ya shiga ɗakin Atika, wacce ita ce matarsa ta farko, domin mata bankwana ya koma ɗakin ɗayar matarsa da suke rayuwa a gida ɗaya.
Rahotanni sun bayyana cewa Salihu ya ware wa kowace mace kwana biyu, kuma ya saba yin bankwana ga kowaccen su idan zai koma wani ɗakin.
Wata majiya a cikin gidan da lamarin ya auku, ta ce:
"Kuma abin da yaje yi kenan a ɗakin da misalin ƙarfe 8:00 na dare, amma Atika ta fusata, ta cije sa a yatsa har ta ji masa rauni."
Mahaifiyar Salihu Hajiya Hauwa Umar ta shaida wa manema labarai yadda abun ya faru, ta ce:
"Ɗayar matar ta yi kokarin cetonsa, ta ɗaure yatsan da uwar gidan ta ciza, amma Atika, wacce ta kulle kofar gidan, ta rike shi ta baya, ta daba masa wuka a wuya ba sau ɗaya ba."
"An kai shi Asibiti inda Likita ya tabbatar da rai ya yi halinsa, kuma tuni aka masa jana'iza kamar yadda musulunci ya tanada, yayin da yan sanda ke tsare da matar."
Matar Aure Mai Ciki Ta Yi Garkuwa Da Kanta, Ta Siya Gida Da Kuɗin Fansar Da Ta Karɓa Daga Hannun Masoyinta Na Facebook
Har yanzun hukumar yan sanda reshen jihar Nasarawa ba ta ce komai ba game da faruwar lamarin.
A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun bindige Hadimin gwamna har Lahira a wurin ta'aziyya
Wasu tsagerun yan bindiga sun tare hadimin gwamnan Taraba, Honorabul Gbashi, sun bindige shi har Lahira.
Wani wanda ke tare da mamacin ya bayyana cewa sun baro wurin Jana'izar da suka halarta yayin da maharan suka tare su.
Asali: Legit.ng