An shiga tsakani: Za a yi tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha yau Litinin

An shiga tsakani: Za a yi tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha yau Litinin

  • Alamu na nuna cewa, kasar Belarus za ta shiga tsakani domin sasanta Rasha da kasar Ukraine a yakin da ya barke
  • Idan baku manta ba, shugaban Rasha ya danno sojojinsa kasar Ukraine a wani shirin farmakin kasar a makon jiya
  • Kasashen biyu za su yi zaman tattaunawar zaman lafiya a yau Litinin a wani yanki na kasar Belarus da ke makwabtaka dasu

Belarus - Rahoton da muka samo daga jaridar Independent ta kasar Burtaniya ya ce, kasar Belarus za ta karbi bakuncin tattaunawar zaman lafiya ta farko tsakanin Ukraine da Rasha a kan iyakarta, kwanaki biyar bayan da Vladimir Putin ya farmaki Ukraine.

Wannan batu na zuwa ne a yau Litinin, 28 ga watan Fabrairu, kasa da mako kenan da mamayar Rasha a kasar Ukraine.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: 'Yan Najeriya sun samu mafaka a kasashe biyu da ke makwabtaka da Ukraine

Tattaunawar Rasha da Ukraine
An shiga tsakani: Za a yi zaman tattaunawar zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha yau Litinin | Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasuwannin kasar Rasha suka fara fuskantar dakansu, inda farashin Ruble na Rasha ya yi kasa a tarihi, sannan bude kasuwar hada-hadar hannayen jari ya jinkirta har zuwa tsakar rana.

A ranar Lahadin da ta gabata shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine ya ce sa'o'i 24 masu zuwa za su kasance masu kunci da muhimmanci ga Ukraine, yayin da yake magana da Boris Johnson ta wayar salula.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mista Johnson ya yi alkawarin tura tallafin sojoji ga al'ummar kasar Ukraine da ke fama da harin makwabciyarta Rasha.

Dakarun Rasha sun bi takaitacciyar hanya cikin dare tare da kai hari kan gine-gine a birnin Kyiv da Kharkiv.

Rahoton Sky News ya ce, hotunan tauraron dan adam sun nuna jerin gwanon sojojin Rasha sama da tsawon mil uku suna kusantar Kyiv a daidai lokacin da shugaban Ukraine ya yi magana game da lokaci mai muhimmanci cikin sa'o'i 24 na ranar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Belarus ta shiga yakin Rasha, tana shirin danna dakarunta cikin Ukraine

Tun da farko a ranar Lahadi shugaba Putin na Rasha ya umarci dakarunsa na nukiliyar Rasha da su kasance cikin shiri domin martani ga abin da ya kira kalamai masu zafi na shugabannin NATO da takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa kasarsa.

Belarus ta shiga yakin Rasha, tana shirin danna dakarunta cikin Ukraine

A wani labarin, a yayin da ake ci gaba da yin Allah wadai da mamayar da kasar Rasha ta yi wa kasar Ukraine, Belarus na shirin tura dakaru domin taimakawa shugaba Vladimir Putin domin yakar Ukraine, in ji rahoton Washington Post.

Shugaban Rasha Vladimir Putin da shugaban Belarus Alexander Lukashenko abokan kawance ne na kud-kud. Rahotanni sun kuma nuna cewa, ana kyautata zaton barin sojojin Belarus zuwa Ukraine a yau Litinin 28 ga watan Fabrairu.

An bayyana hakan ne jim kadan bayan da wata kuri'ar raba gardama a Belarus ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda ya rushe matsayin kasar na kasancewa mara hulda da nukiliya - hakan na nufin kasar za ta iya daukar nauyin makaman Rasha.

Kara karanta wannan

Shahararren biloniyan Japan, Mikitani, ya gwangwaje Ukraine da tallafin $8.7m

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

iiq_pixel