Babbar Magana: Yan bindiga sun bindige Hadimin gwamna har Lahira a wurin ta'aziyya

Babbar Magana: Yan bindiga sun bindige Hadimin gwamna har Lahira a wurin ta'aziyya

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun tare hadimin gwamnan Taraba, Honorabul Gbashi, sun bindige shi har Lahira
  • Wani wanda ke tare da mamacin ya bayyana cewa sun baro wurin Jana'izar da suka halarta yayin da maharan suka tare su
  • A halin yanzun dakarun sojoji sun bazama cikin daji domin nemo gawar mutumin, bayan sun yi gaba da ita

Taraba - Yan bindiga sun halaka Honorabul Levi Gbashi, hadimin gwamnan jahar Taraba, Darius Ishaku, a karamar hukumar Donga dake jahar.

Wani shaidan gani da ido, Mista Tortsua Naagh, ya shaida wa wakilin Leadership cewa lamarin ya auku a ƙauyen Ityopaa, yayin da marigayin ke gab da barin wurin jana'izar da ya halarta.

Yan bindiga
Babbar Magana: Yan bindiga sun bindige Hadimin gwamna har Lahira a wurin ta'aziyya Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Shaidan ya ce:

"Muna shirin barin wurin bikin jana'izar a cikin Mota lokacin da yan ta'addan suka tare mu, suka umarci mu sa guiwowin mu a ƙasa."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa Da Sarki a Jihar Arewa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muka ƙi bin umarnin su domin jawo hankalin mutanen dake kusa da wurin, ɗaya daga cikin su ya bude wa Honorabul Gbashi wuta, nan take ya rasa rayuwarsa."
"Ya juyo kaina sai bindigan ta ƙage. Yayin da ya je nemo wata bindiga daga ɗan uwansa sai na gudu na shiga cikin dandazon mutanen da suka halarci bikin jana'iza."

Ya ƙara da cewa duk da haka sai da ya biyo baya domin nemo inda na bace, amma Allah ya taimake ni na tsira daga sharrinsa a wurin.

Yan bindigan sun tafi da gawarsa

Mutumin ya ce yan bindigan sun ɗauki gawar marigayin, kuma suka tafi da ita zuwa cikin jeji.

Shugaban ƙaramar hukumar Donga, Honorabul Nashuka Ipeyen, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa ya kira jami'an tsaron dake yankin.

"Eh, abun babu daɗi, lamarin ya auku, na yi magana da kwamandan dakaru na musamman, kuma ya tura jami'an zuwa yankin nan take."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani ma'aikacin jami'a ya mutu a cikin ruwan shakatawa a Hotel

"Yanzu haka, Sojoji sun bazama cikin jeji domin nemo gawar hadimin gwamnan da kuma kame maharan."

Kakakin hukumar yan sanda na jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya shaida mana cewa ba shi da masaniya kan faruwar lamarin amma zai bincika.

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya dira Faris ziyarar mako biyu ana tsaka da yakin Ukraine da Rasha

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zai halarci taron zaman lafiya a Farisa, wanda aka shirya gudanarwa ranar 11 ga watan Maris.

Domin samun halartar taron na duniya, shugaban ƙasa ya bar fadarsa Aso Villa ranar 26 ga watan Fabrairu, 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262