Ra'ayi: Dr Ahmed Gumi ya yi tsokaci kan labarin cewa Gwamnatin Zamfara zata kashe kudi don taron Maulidi

Ra'ayi: Dr Ahmed Gumi ya yi tsokaci kan labarin cewa Gwamnatin Zamfara zata kashe kudi don taron Maulidi

Sheikh Dr Ahmad Mahmud Gumi, ya bayyana ra'ayinsa kan wani labari dake cewa Wai Gwamnatin Zamafara zata kashe miliyoyin kudi domin Taron Maulidi na biyu a cikin shekara daya.

A jawabin da ya wallafa a shafin na Facebook ranar Lahadi Sheikh Gumi yace:

Wai Gomnatin Zamafara zata kashe miliyonin kudi domin Taron Maulidi na biyu acikin shekara daya.
In haka gaskiya ne, to wanan haramun ne koma almubazzaranci ne da kudin jamaa.

Na daya, kudin jamaa kudin gina musu makarantu ne da asibitai, da samar da ruwan sha, da hanyuyi, da sulhu tsakanin mutane, ba kudin yada akidar bangarenci bane da raba kan mutane da gurbata wa mutane addininsu.

Allah Madawkaki Yana cewa:

{لَا خَيْرَ فِي كَثِيرٍ مِنْ نَجْوَاهُمْ إِلَّا مَنْ أَمَرَ بِصَدَقَةٍ أَوْ مَعْرُوفٍ أَوْ إِصْلَاحٍ بَيْنَ النَّاسِ وَمَنْ يَفْعَلْ ذَلِكَ ابْتِغَاءَ مَرْضَاتِ اللَّهِ فَسَوْفَ نُؤْتِيهِ أَجْرًا عَظِيمًا } [النساء: 114]

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Rikici ya barke a mahaifar shugaba Buhari Daura kan wanda za'a ba takara a APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu, fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka, kõ kuwa wani sanannen alhẽri, kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin nẽman yardõdin Allah, to, zã Mu bã shi lãda mai girma.”

A gaskiya, Zamfara na cikin jihohin da sukafi kowace fuskantar kalubalen jahilcin addini da ilimin zamani, inda Imani da tasfe-tsafe yayi kaka gida. Tana cikin jihohin da mutanenta suka fi kowane talauci da rashin biyan bukatu duk da arzikin da Allah ya shinfida a cikin kasar. Tana cikin jihohin da suka fi kowace rashin kwancinyar hankili da taadanci, tana cikin jihohin da suka fi kowace tarurrukan bashi, da karancin albashi ga maikatanta.

Tana cikin jihohin da suke da masalar muguwar gaba da kiyayya ta siyaya domin jahilcin mutane da Yan siyarsa kansu.

Kara karanta wannan

2023: Matashin ɗan takara dake son gaje kujerar Buhari ya shiga jihar Neja, ya nemi albarkar IBB

Shin a irin wannan hali, hankali ma ba zai amince da shigar da bangarancin addini cikin irin wannan taasar da kasar ke ciki ba.

Inde Zamafara baza ta tallafa ba wajen yada sunnar da duniya tayi ittifaki akanta ba kamar Shariah a shekarun baya, to kada ta yada abunda duniya suka yarda bidiaa ne (da masu cewa maikyau ce ko marassa kyau ce, duk sun yadda bidiaa ce).

Lalle, a Zamfara siyasa ta kusa ta zama sababin raba kan jamaa da almubazzaranci da kudi da dukiyar jamaa. Dole siyasar ta sake salo.

Allah Ya sawkake! Amin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng