Mayakan ISWAP sun kashe mutane takwas, sun kona wani kauye a Borno

Mayakan ISWAP sun kashe mutane takwas, sun kona wani kauye a Borno

  • Yan ta'addan ISWAP sun farmaki kauyukan Mandaragirau da Ghuma da ke karamar hukumar Biu ta jihar Borno
  • Harin wanda suka kai a daren ranar Asabar, 26 ga watan Fabrairu, ya yi sanadiyar kashe mutane takwas tare da jikkata wasu
  • Maharan sun kuma kona wasu shaguna, suka sace kayan abinci da dabbobin jama'a

Borno - Mayakan kungiyar ta’addanci ta ISWAP sun kashe akalla mutane takwas a wani hari da suka kai karamar hukumar Biu ta jihar Borno.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa mayakan sun farmaki kauyukan Mandaragirau da Ghuma da ke karamar hukumar a daren ranar Asabar, 26 ga watan Fabrairu, inda suka kashe mazauna takwas da kuma jikkata wasu.

An tattaro cewa wasu majiyoyi na rundunar soji ta dakile wani hari da ISWAP suka kai hanyar Mandaragarau a safiyar Asabar.

Kara karanta wannan

Borno: Mayakan ta'addancin ISWAP sun sheke rayuka 5 Kautikari a sabon hari

Mayakan ISWAP sun kashe mutane takwas, sun kona wani kauye a Borno
Mayakan ISWAP sun kashe mutane takwas, sun kona wani kauye a Borno Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: UGC

An tattaro cewa rundunar sojin Najeriya, karkashin Operation Desert Sanity, da ke sintiri mai dogon zango a yankin, sun datse sadarwar ‘yan ta’addan da ke aikin dasa bama-bamai a kan hanyoyin tare da kai farmaki kan sansanin sojoji.

Amma sai dakarun suka farmaki wajen sannan suka yi maganin da yan ta’addan.

Biyo bayan datsewar, sai yan ta’adda tara kan babura uku suka farmaki kauyukan Mandaragirau da Ghuma, inda suka zargi mazauna kauyukan da yiwa sojoji kwarmaton shirinsu.

Rahoton ya kara da cewar maharan sun kuma kona wasu shaguna, suka sace kayan abinci da dabbobin mazauna garuruwan.

Sojoji sun dakile harin ta'addanci a yankin Konduga

Dakarun dun yi nasarar dakile wani hari da kungiyar ta ISWAP suka kai karamar hukumar Konduga.

Majiyoyi sun ce maharan sun yi yunkurin kai hari sansanin sojoji a hanyar Bama, lokacin da suka hadu da da turjiya daga sojojin da ke wurin.

Kara karanta wannan

Niger: 'Yan ta'adda sun kai sabon farmaki, sun halaka rayuka 17, ciki har da uba da 'dansa

Borno: Mayakan ta'addancin ISWAP sun sheke rayuka 5 Kautikari a sabon hari

A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa akalla rayukan mutane biyar ne suka salwanta a ranar 25 ga watan Fabrairu, yayin da mayakan ISWAP suka yi kokarin kaiwa unguwan Kautikari, kusa a Chibok a arewa maso gabashin Najeriya hari.

HumAngle ta ruwaito, kamar yadda wani mazauni yankin ya bayyana, 'yan ta'addan sun doshi anguwan bayan wucewa ta kauyen Lassa a yankin Askira Uba da kauyen Shawa, kilomita kadan daga Chibok, kafin aukawa Kautikari tsakanin karfe 5:00 zuwa 6:00 na yammacin ranar Juma'a.

An ruwaito yadda mafarauta suka dakile harin 'yan ta'addan ta hanyar fada da bakin wuta, bayan kai samamen. Sai dai, sun yi nasarar kunna wutar yakin kafin sojojin su iso, gami da fatattakar 'yan ta'addan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng