Da duminsa: Tsohon shugaban masu rinjaye a majalisar Gombe ya sauya sheka daga APC
- Jam'iyyar APC na cigaba da rashin mambobi a majalisar dokokin jihar Gombe makonnin nan
- Wannan ya biyo bayan sulhun da aka tsakanin Gwamnan jihar da tsohon Gwamna Danjuma Goje
- Yan majalisan da suka sauya sheka cun akwai sauran yan majalisa da suka yanke shawarar fita daga APC
Ruwan sauya sheka daga jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Gombe ya dau sabon salo yayinda tsohon shugaban majalisar dokokin jihar, Markus Samuel, ya sanar da fitarsa.
Sauya shekara Marcus Samuel ya biyo bayan sauya shekar wani mamban majalisar, Rambi Ibrahim cikin makon nan, rahoton TheNation.
Wata majiya dake kusa yan majalisan ta bayyana cewa ai da sannu akwai yan majalisar APC da dama da ke niyyar sauya shekar.
A cewar majiya, yanzu akwai yan majalisa biyar da suka yanke shawarar fita daga APC.
Markus Samuel ya tabbatar da labarin sauya shekarsa ta wayar tarho.
Yace:
"Tuni na kira mai girma Gwamna don sanar masa halin da nike ciki da kuma dalilin da yasa na fita daga jam'iyyar."
A cewarsa, akwai karin yan majalisa APC cikin 20 dake majalisar da zasu sanar da fitarsu daga jam'iyyar kwanan nan.
Tsohon Kwamishina, Hadimin gwamna da wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC
A wani labarin kuwa, manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP da suka yi aiki a gwamnatin tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, sun sauya sheka zuwa APC mai mulki.
Leadership ta rahoto cewa manyan mutanen da suka sauya shekan sun haɗa da, tsohon kwamishina, Babagoro Hashidu, da tsohon mashawarci na musamman, Alhaji Maigari Malala.
Kazalika sun koma APC tare da fitaccen ɗan siyasa kuma mai faɗa aji a siyasar PDP ta karamar hukumar Kwami, Alhaji Kari Daba.
Fitattun yan siyasan guda uku sun ziyarci gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, inda suka tabbatar da mubaya'ar su kuma suka shigar da gaisuwar girma.
Asali: Legit.ng