Farfesa Osinbajo ya yi wa tubabbun mayakan Boko Haram alkawarin sabuwar rayuwa

Farfesa Osinbajo ya yi wa tubabbun mayakan Boko Haram alkawarin sabuwar rayuwa

  • Gwamnatin tarayya ta ɗauki alkawarin inganta rayuwar tubabbbun mambobin Boko Haram su tsaya da kafafunsu
  • Farfesa Yemi Osinajo ya ce gwamnati ta shirya samar wa tubabbun hanyoyin kudin shiga na halak da wurin zama
  • Gwamna Zulum ya yi kira ga gwamnati ta taimaka musu wajen kammala maida yan gudun hijira gidajen su

Borno - Mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya tabbatarwa tubabbun mambobin Boko Haram cewa gwamnatin tarayya zata taimaka musu.

Daily Trust ta rahoto cewa Osinbajo ya alkawarta wa tubabbun yan ta'addan cewa gwamnatin zata sama musu hanyoyin kuɗin shiga na halak domin su fara sabuwar rayuwa.

Yan ta'addan da suka miƙa wuya sun yi wa Osinbajo kyakkyawar tarba yayin da yakai musu ziyara a sansanin mahajjata dake Maiduguri ranar Alhamis.

Farfesa Osinbajo da gwamna Zulum
Farfesa Osinbajo ya yi wa tubabbun mayakan Boko Haram alkawarin sabuwar rayuwa Hoto: The Governor of Borno state/facebook
Source: Facebook

Mataimakin shugaban ƙasan ya kai ziyarar aiki jihar Borno ne domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Zulum ta kammala.

Kara karanta wannan

Ya kamata a ba mutanen Legas tikitin shiga Aljanna kyauta sabida wahalar cunkoso, inji Malam El-Rufa'i

Osinbajo ya ce:

"Ni ne shugaban kwamitin da gwamnati ta kafa, kuma mai girma gwamnan Borno, Babagana Zulum, shi ne mataimakin shugaba."
"Zamu yi aiki tare da ku, gwamnatin jiha, da hukumomin bada tallafi domin samar muku da abubuwan rayuwa, ba kuɗin shiga kaɗai ba, har da wurin da zaku zauna da iyalanku, ku cigaba da harkokin kasuwanci."
"Amma wajibi sai kun yi aiki da hakuri. Allah ya muku albarka, kuma ina muku fata nagari. Zamu yi iya bakin kokarin mu wajen kula da ku da izinin Allah."

Muna bukatar taimakon FG - Zulum

Gwamna Zulum ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta taimaka wa gwamnatinsa a kokarin da take na maida yan gudun hijira gidajen su.

Ya kuma jaddada bukatar kulawa da tubabbun yan Boko Haram yadda ya kamata cikin kula da tsanaki, ya ce:

"Idan muka iya canza mayakan Boko Haram da suka miƙa wuya, to nan gaba kaɗan ayyukan ta'addanci za su zama tarihi."

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Gwamna El-Rufa'i ya fadi gaskiyar dalilin cire ɗansa daga makarantar gwamnati

A wani labarin na daban kuma Gwamna El-Rufa'i ya fadi gaskiyar dalilin cire ɗansa daga makarantar gwamnati

Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana cewa wasu sun fara kulla-kullan sace ɗansa shiyasa ya cire shi daga makaranta.

Gwamnan ya ce ba wai yana tsoron zasu samu nasara bane, baya son sauran dalibai rayuwar su ta shiga hatsari kan ɗansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262