Da Ɗumi: Kotun Ɗaukaka Ta Rage Wa Farouk Lawan Adadin Shekarun Da Aka Yanke Masa a Gidan Yari

Da Ɗumi: Kotun Ɗaukaka Ta Rage Wa Farouk Lawan Adadin Shekarun Da Aka Yanke Masa a Gidan Yari

  • Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke wa tsohon dan majalisa, Farouk Lawan, hukuncin bayan gamsuwa da cewa ya amshi rashawar $500,000 a 2012
  • An yanke wannan hukuncin ne a ranar Alhamis bayan kotun ta wanke dan majalisar daga laifuka biyu da aka daure shi akan su a watan Yunin da ya gabata
  • Dak yar kotun ta amince da wannan hukuncin sannan ta rage masa lokacin da zai yi a gidan gyaran halin, daga shekaru 7 zuwa shekaru 5

Abuja - Kotun daukaka kara da ke Abuja ta tabbatar da daurin tsohon dan majalisa, Faruk Lawan bisa kama shi da laifin amsar rashawar $500,000 lokacin cire tallafin man fetur a 2012, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Bugagge ya zuba omo a ledar ruwan maganin majinyaci, ya gamu da fushin alkali

Sai dai da kyar alkalin ya amince da hukuncin bayan an wanke shi daga laifuka biyu da aka zargin shi da aikatawa har wata kotu ta daure shi a watan Yunin shekarar da ta gabata.

Da Ɗumi: Kotun Ɗaukaka Ta Rage Wa Farouk Lawan Adadin Shekarun Da Aka Yanke Masa a Gidan Yari
Kotun Ɗaukaka Ta Rage Wa Farouk Lawan Adadin Shekarun Da Aka Yanke Masa a Gidan Yari. Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

An rage wa Lawan lokacin da zai yi a gidan yari, inda zai yi shekaru 5 a maimakon 7.

Wannan ya biyo bayan wanke shi da aka yi daga laifuka biyu na baya inda ya kamata ya yi shekaru 7 a gidan yari.

Kotun ta tabbatar da daurin nasa akan laifi daya da ya aikata wanda kotun baya ta yanke masa shekaru 5 a gidan gyaran hali, rahoton Premium Times.

Yayin da kotu ta yi watsi da laifuka biyu na baya, kwamitin mutane uku wacce babban alkalin kotun, Monica Dougan-Mensem ta jagoranta, ta yanke hukunci akan cewa an kasa samar da kwakkwarar hujjar da za ta tabbatar da cewa Lawan ya bukata kuma ya amince da amsar dala miliyan 300 daga biloniya Femi Otedola don cire kamfanin dan kasuwar daga jerin kamfanonin da ake zargin sun yi ha’inci a tallafin man fetur na 2012.

Kara karanta wannan

Shiga tashin hankali: Abba Kyari da jiga-jigai 6 da suka fada rashin lafiya yayin bincikarsu

Kotu ta amince da cewa Faruk ya amshi rashawar $500,000

Sai dai kotun daukaka kara ta tsaya akan hukunci da kotun kasa ta yanke na cewa lallai Lawan ya amshi $500,000 daga hannun Otedola. Hakan yasa kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 5 a gidan yari.

Kotun daukaka kara ta tsayi akan cewa daga hukuncin har daurin da kotun baya ta yi, amma ta wanke shi daga sauran laifuka biyu da aka zarge shi na nema da kuma amincewa da amsar dala miliyan 3 daga Otedola.

Bayan kwashe shekaru 9 ana shari’a, alkalin da ya yanke hukuncin, Angela Otaluka, na babbar kotun tarayya, Abuja, ta yanke wa tsohon dan majalisar hukunci bisa yakinin ya aikata laifuka uku.

Ta yanke wa Lawan hukunci saboda aikata rashawa, bukatar rashawar dala miliyan 3 da kuma amsar rashawar dala dubu dari biyar daga hannun dan kasuwar don aikata ha’inci a tallafin fetur a 2012.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164