Da Dumi-Dumi: Jirgin Yaƙin Sojojin Ukraine Ɗauke Da Mutum 14 Ya Yi Haɗari Kusa Da Kyiv
1 - tsawon mintuna
Ukraine - Wani jirgin yaki na sojojin Ukraine dauke da mutane 14 ya fadi ya yi hatsari a kusa da kudancin Kyiv a ranar Alhamis, a cewar hukumar ayyukan gaggawa, rahoton The Punch.
Hukumar ta ce har yanzu "tana nazarin adadin mutanen da suka mutu."
Lamarin ya faru ne a misalin kilomita 20 da kudancin Kyiv, a yayin da rahotanni ke nuna cewa ana kai hare-hare a wasu yankunan birnin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng