Ngige: Ba don kwarewar mulkin Buhari ba, da yanzu 'yan Najeriya suna neman mafaka a Nijar da Kamaru
- Ministan kwadago, Chris Ngige, ya ce da a ce ba kwararre kuma jajirtacce irin Buhari ne ke mulkin Najeriya ba, da yanzu kasar ta zama tamkar Venezuela
- A cewar ministan yayin da yake karbar lambar yabo da girmamawa ta INSLEC a Abuja, ya ce da babu Buhari da yanzu 'yan Najeriya sun tafi gudun hijira a Nijar da Kamaru
- Ministan ya sanar da cewa duk da kasar nan ta na cikin matsaloli, ba laifin gwamnatin Buhari ba ce, rashin tsarin baya ne yake farautar jama'a
FCT, Abuja - Chris Ngige, ministan kwadago, ya ce da a ce ba a samu jajirtaccen mulki irin na shugaban kasa Muhammadu Buhari ba, da yanzu 'yan Najeriya sun zama 'yan gudun hijira a Kamaru da Nijar.
TheCable ta ruwaito cewa, Ngige ya sanar da hakan ne a ranar Laraba bayan an bashi digirin girmamawa a INSLEC a Abuja.
Ministan ya kara da cewa, da babu gogewar mulki irin ta Buhari, da yanzu kasar nan ta kasance cikin rikici kamar Venezuela.
Venezuela ta na fama da matsalar rashin daidaiton siyasa da na tattalin arziki a cikin shekarun da suka gabata. Kasar ta ga tabarbarewa a fannin kiwon lafiya, abinci, wutar lantarki da rashin man fetur wanda a hankali suke ta'azzara, lamarin da yasa jama'a ke ta gudun hijira da neman mafaka.
Kamar yadda Ngige yace, duk da Najeriya na fama da wasu matsalolin, ba laifin gwamnati mai ci a yanzu bane, kawai rashin tsari ne a shekarun da suka gabata inda ya kara da cewa shugabanci nagari ya na da matukar muhimmanci a kowacce al'umma.
"Shugaba nagari dole ya zamanto mutum mai aiwatarwa. Dole ya zama mai ilimi saboda baya da hangen nesa, ya dace ya kasance mai rarrabewa da gyarawa. Ya kasance zakakuri a komai," yace a wata takarda da Charles Akpan, mataimakin daraktan yada labarai na ma'aikatar kwadago yasa hannu.
“Ba dole bane ya kasance kwararre a komai ba, amma ya kasance ya kware a wurare masu yawa. Dole ne ya kasance mai kwarin guiwar tabbatar da manyan hukunci. Idan ba a tabbatar da abubuwa cike da kwarin guiwa, wasu za su mutu ko kuma su tafi ba a more su ba."
Majalisar Najeriya za ta sa baki domin Kungiyar ASUU ta janye yajin-aiki, a bude Jami’o’i
A wani labari na daban, majalisar wakilan tarayya ta bukaci gwamnatin tarayya da kungiyar ASUU su yi aiki da yarjejeniyar MoU da aka sa hannu a wajen shawo kan sabaninsu.
Kamar yadda Channels TV ta fitar da rahoto, ‘yan majalisar tarayyan sun nemi gwamnati da malaman jami’an su sasanta domin albarkacin daliban kasar nan.
A zaman da majalisar tayi a ranar Talata, 22 ga watan Fubrairu 2022, an bukaci kwamitocin kwadago da na ilmi a majalisar ya sa baki a kan batun yajin-aikin.
Asali: Legit.ng