Ina tare da dalibai mata Musulmai, babu wanda ya isa ya hanasu sanya Hijabi: Gwamnan Kwara

Ina tare da dalibai mata Musulmai, babu wanda ya isa ya hanasu sanya Hijabi: Gwamnan Kwara

  • A karshe, Gwamna AbdulRazak na Kwara ya bayyana matsayarsa kan dambarwan Hijabi dake gudana a jihar
  • Akalla mutum daya ya rasa rayuwarsa ranar da zange-zanga ya barke a karamar hukumar Oyun ta jihar
  • Shugabannin makarantun Mission dake jihar sun lashi takobin hana dalibai mata sanya Hijabi duk da hukuncin kotu

Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya bayyana cewa ko shakka babu yana tare da dalibai mata Musulmai kan lamarin sanya Hijabi cikin makarantun jihar.

Yace wannan ita ce matsayarsa saboda shari'o'in da kotu ta yanke kan lamarin da kuma kasancewar Kwara jiha mai daidaito tsakanin addinai kuma jihar da tafi kama da kudu wajen adadin masu addinai mabananta.

Abdulrazaq yace gwamnatinsa kawai doka da gaskiya take bi da kuma nuna adalci tsakanin kowa, sakataren yada labaransa, Rafiu Ajakaye, ya bayyana, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Duk wanda yayi mana shisshigi kan yakinmu da Ukraniya zai fuskanci ukuba, Shugaban kasan Rasha

Gwamnan Kwara
Ina tare da dalibai mata Musulmai, babu wanda ya isa ya hanasu sanya Hijabi: Gwamnan Kwara
Asali: UGC

Wannan jawabi na Gwamna ya biyo bayan tuhume-tuhumen da Musulmai da Kirista ke yi cewa Gwamnan ya ki bayyana ra'ayinsa kan lamarin saboda siyasa.

Tuni dai iyalan Habeeb Idris, dalibin da aka kashe yayin zanga-zanga a makarantar Oyun Baptsit kwanakin baya sun yi watsi da diyyar N1m da gwamnatin jihar ta basu.

Hakazalika mutum 11 da suka jikkata sun yi watsi da kudi N250,000 da gwamnatin jihar ta basu.

Rikicin Hijab a Kwara: Iyalan wanda aka kashe sun nemi a biya su diyyar N113m

Iyalan Habeeb Idris wanda aka kashe a lokacin rikicin Hijabi a makarantar Oyun Baptist High School, Ijagbo da wasu Musulmai a jihar Kwara sun nemi N113, 388,000 a matsayin diyyah daga gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Yan bindiga sun halaka babban jami'in Kwastam a garin Kaduna

Da farko Musulman da iyalan sun mayar da naira miliyan daya da gwamnati ta baiwa iyayen marigayin a lokacin wata ganawa da sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Mamman Jibril, Daily Trust ta rahoto

Hakazalika Musulmai 11 da aka jiwa munanan raunuka a yayin harin suma sun dawo da N250,000 da gwamnatin jihar Kwara ta basu ta hannun Abdullahi Abubakar da Taofeeq Mustafa (wanda abun ya ritsa da shi) a madadin al’umman Musulmai na Offa/Oyun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng