An Yi Ƙarar Wata Mata Saboda Lakaɗa Wa Maƙwabcinta Duka Bayan Ta Mallake Masa ‘Kitchen’

An Yi Ƙarar Wata Mata Saboda Lakaɗa Wa Maƙwabcinta Duka Bayan Ta Mallake Masa ‘Kitchen’

  • An gurfanar da wata mata mai shekaru 49, Abosede Oloyede a gaban kotu a Legas kan zarginta da lakawa da makwabcinta duka da tada zaune tsaye
  • Mai gabatar da kara ya shaida wa kotu cewa Oloyede ta mallake wa makwabcinta, Isiaka Baruwa, dakin girkinsa ne kuma da ya yi magana ta masa duka
  • Bayan karanto mata tuhumar, wacce aka yi karar ta musanta aikata laifin da ake zargin ta da aikatawa, daga nan aka bada belinta aka dage cigaba da sauraron karar

Legas - Wata mata mai shekaru 49, Abosede Oloyede, da aka ce ta kwace wa makwabcinsa 'kitchen' wato dakin girki, ta gurfana a gaban Alkalin Kotun Majistare na Surelere Lagos a ranar Laraba.

Ana tuhumar Oloyede, mai zaune a gida mai lamba 11 Shobowole St. Itire Surulere Lagas bisa laifin tada zaune tsaye da duka, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Rayuwar aure: Yadda wata kotu ta gimtse auren da yayi shekaru 7 saboda sabani tsakanin ma'aurata

An Yi Ƙarar Wata Mata Saboda Lakaɗa Wa Makwabcinta Duka Bayan Ta Mallake Masa ‘Kitchen’
An Yi Ƙarar Wata Mata Saboda Dukan Makwabcinta Bayan Ta Mallake Masa ‘Kitchen’. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yadda abin ya faru

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeta Courage Ekhuerohan ya shaida wa kotu cewa Oloyede ta aikata laifukan a cikin watan Janairu a gida mai adireshin da aka ambata.

Ya yi zargin cewa Oloyede ta bar inda ta ke haya ta yi babakere a wani 'kitchen' a cikin gidan na su na haya.

Ya ce mai kitchen din, wani Mr Isiaka Baruwa, ya tuntubi Oloyede domin ta dena masa amfani da kitchen, daga nan sai ta lakada masa duka.

Laifin ya ci karo da sashi na 168 da 173 na dokar masu aikata laifi na Jihar Legas ta shekarar 2015.

Wacce ake zargi ta musanta aikata laifin

Amma, Oloyede ta ce bata amsa laifin da ake tuhumar ta da aikatawa ba.

Kara karanta wannan

Karfin hali: An yi cacar baki tsakanin mai Shari'a da Nnamdi Kanu kan tufafinsa

Alkalin kotu, M.I. Dan-Oni, ta bada belin Oloyede kan kudi N5,000 tare da mutum daya da ya tsaya mata.

Ta dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 10 ga watan Maris.

Kano: Ya Jefa Yaro Cikin Rijiya Bayan Yin Rikici Da Mahaifin Yaron, Kotu Ta Ce a Tsare Shi a Gidan Gyaran Hali

A wani labarin, Alkalin kotun Majistare da ke zamanta a Kano, a ranar Juma'a, ya bada umurnin a tare wani mutum mai shekaru 33, Abubakar Aminu, a gidan gyaran hali kan zarginsa da jefa yaro dan shekara hudu, Abdulmalik Suleiman cikin rijiya.

An tuhumar wanda aka yi karar, mazaunin Rijiyar Lemo Quaters a Kano da laifin yunkurin aikata kisa kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Mai gabatar da karar, Asma'u Ado, ta sanar da kotu cewa wani Aminu Suleiman mazaunin Bachirawa Quaters, a Kano ne ya kai rahoton afkuwar lamarin a ofishin yan sanda na Rijiyar Lemo a Kano a ranar 14 ga watan Oktoban 2021.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164