Rayuwar aure: Yadda wata kotu ta gimtse auren da yayi shekaru 7 saboda sabani tsakanin ma'aurata
- Wata kotun Jos ta gimtse auren shekaru bakwai saboda wani sabani da ya gifta tsakanin Ma'aurata
- Matar mai suna Sumaiya Muhammad ta yi karar mijinta, Bala Usman, cewa ya kaurace mata tsawon shekaru da ta yi tana jinya a gidan iyayenta, kuma baya daukar dawainiyarsu
- Da yake zartar da hukunci, Alkalin kotun, Ishaq Danjuma, ya nemi Sumaiya ta mayarwa da Usman N50,000 da ya biya a matsayin sadakinta
Plateau - Wata kotun Jos da ke zama a Nassarawa Gwong, ta raba auren shekara bakwai tsakanin Sumaiya Muhammad da mijinta, Bala Usman, kan hujjar kauracewa juna.
An warware auren mata da mijin ne a ranar Laraba, 23 ga watan Fabrairu.
Alkalin kotun, Ishaq Danjuma, da yake aiwatar da bukatar Sumaiya ya ce duk kokarin da aka yi domin sasanta ma’auratan ya ci tura, jaridar Punch ta rahoto.
Alkalin ya umurci mai karar da ta mayarwa wanda ake kara N50,000 na sadaki da Usman ya biya bayan an yi masu Khu’I kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
Danjuma ya kuma baiwa wacce ke kara ikon rike yaran da suka haifa a auren.
Sai dai kuma ya ce wanda ake karan na da damar ziyartan yaransa a lokutan da suka dace na rana ba tare da shamaki ba.
Da farko dai Sumaiya ta roki kotu da ta raba auren, cewa mijinta ya kaurace mata a lokacin da take rashin lafiya da kuma zauna tare da iyayenta.
Sumaiya ta zargi Usman da kin daukar dawainiyar iyalin tsawon shekaru uku da ta yi tana jinya, rahoton Daily Post.
Kotu ta garkame magidanci a gidan yari bayan ya kara aure babu amincewar uwargidansa
A wani labarin, wata kotu da ke zama a kasar Pakistan ta aike wani magidanci zuwa gidan yari sakamakon kara aure na biyu da yayi babu amincewar uwargidansa.
Kotun da ke zama a lardin Lahore ta yi fatali da ikirarin magidancin mai suna Shahzad Saqib na cewa addininsa na Musulunci ya bayar a damar ya kara aure, Aminiya Daily Trust ta rahoto.
Matar Saqib mai suna Ayesha Bibi, ta samu nasara a kotun bayan da ta yi ikirarin cewa kara auren da yayi babu amincewarta ya ki duba dokokin iyali na kasar Pakistan, al'amarin da yasa kotun ta ci tarar Saqib dala dubu biyu.
Asali: Legit.ng