Labari mai zafi: Majalisar dokokin Zamfara ta tsige mataimakin gwamna daga kujerarsa
- Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa, majalisar dokokin jihar ta tsige mataimakin gwamna, Aliyu Gusau
- Wannan na zuwa ne bayan da majalisar ta karbi rahoton bincike kan tuhume-tuhumen da ake yiwa mataimakin gwamnan
- Gusau dai ya fara samun matsala da gwamnatin jihar Zamfara ne tun bayan da gwamnan jihar ya koma jam'iyyar APC mai mulki
Gusau, Zamfara - Gidan talabijin na TVC ya rahoto cewa, yanzu labari ya shigo cewa, mataimakin gwamnan jihar Zamfara ya rasa kujerarsa bayan da majalisar dokokin jihar ta zauna a yau Laraba.
Wannan na zuwa ne sa'o'i kadan bayan da kwamitin tsige mataimakin gwamnatin ya mika rahoto ga majalisar dokokin jihar, kamar yadda rahotanni suka kawo a baya.
Kwamitin na mutum bakwai da aka kafa domin binciken laifuffukan da ake zargin mataimakin gwamnan a karkashin jagorancin Mai shari’a Halidu Soba mai ritaya, ya mika rahotonsa ga majalisar dokokin jihar, inji gidan talabijin na Channels.
Majalisa ta karbi rahoton bincike
Kakakin majalisar, Nasiru Mua’zu ne ya karbi rahoton da mai shari’a Soba ya gabatar a harabar majalisar da ke Gusau, babban birnin jihar.
Wani mamba a kwamitin Oladipo Okpeseyi ya shaidawa shugaban majalisar cewa, kwamitin ya gudanar da aikinsa cikin tsanaki tare da binciko cikakken gaskiya.
A cewarsa, kwamitin ba shi da ikon yin magana a kan rahoton ko bai wa wani mutum damar yin magana, kamar yadda kundin tsari ya tanada.
Okpeseyi, SAN, ya ce kwamitin binciken ya fitar da kwafi biyu ne kawai na rahoton kuma ya ziyarci harabar majalisar domin gabatar da rahoton ga shugaban majalisar.
A nasa jawabin, Nasiru Mua’zu ya yi alkawarin yin aiki da rahoton kamar yadda kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 ya tanada (wanda aka yi wa kwaskwarima).
Da Dumi-Dumi: Kotu ta bada umarnin kwace kadarori 10, da kudaden Banki na tsohon gwamnan Zamfara
A wani labarin, Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ta bada umarnin wucin gadi na kwace kadarori kusan 10, da makudan kudin dake makare a Banki da ake zargin mallakin tsohon gwamna, Abdul'aziz Yari ne.
Mai shari'a Obiora Egwuatu, shi ne ya bada umarnin yayin yanke hukunci kan bukatar lauyan hukumar yaki da ayyukan cin hanci mai zaman kanta (ICPC), Osuobeni Ekoi Akponimisingha.
Alkalin Kotun ya ce umarnin na wucin gadi zai dauki tsawon watanni biyu ne kacal, kamar yadda Jaridar The Nation ta ruwaito.
Asali: Legit.ng