Muna shirin karban sabon bashin $3bn don kammala wasu ayyuka 10, Ministar Kudi
- Gwamnatin Shugaba Buhari ta bayyana wasu ayyukan da take son yi kafin karewar wa''adinta a 2023
- Sakamakon haka Ministar kudi ta bayyana adadin kudin ake son karban bashi don wadannan ayyuka
- Yan Najeriya da maana tattalin arziki na jan kunnen gwamnati kan yawaitan karban basussuka
Ministar kudi, kasafin kudi, da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin rattafa hannu kan sabon bashin $3.387 billion don yin wasu ayyuka 10 a fadin tarayya.
Ministar ta bayyana hakan a taron da ma'aikatar labarai da al'adu ta shirya kan nasarorin da Gwamnatin tarayya ta samu kan manyan ayyukan cigaba, rahoton Tribune.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta ce gwamnatin Shugaba Buhari ya aiwatar da wasu manyan ayyukan da zasu amfani al'ummar Najeriya.
Tace:
"A 2022 kadai, muna shirin kashe N1.42 trillion kan manyan ayyuka kuma N2.11 trillion kan gina mutane."
Tace ayyukan da za'a aiwatar da sabon bashin sun hada da ginin layin dogon cikin birnin Kano, ginin titin garin Lafiya, jihar Nasarawa, fadada titin 9th Mile (Enugu)-Otukpo-Makurdi, dss.
Ministan ayyuka da gidaje kuwa, Babatunde Fashola, a jawabin da ya bayyana cewa gwamnatin nan ta bada kwangilolin ayyuka 1,019 na gadoji da tituna.
Ministan yace ana ginin gidaje a jihohi 34 da sabbin sakataroyoyi a Anambra, Nasarawa, Bayelsa, Zamfara, Osun da Ekiti.
China ta fara jinkirta bashi, amma gwamnati na neman rancen N5.9tr
Yayin da Sin ke sanya wajen ba gwamnatin Buhari bashi, gwamnatin tarayya na karkata zuwa kasuwannin Biritaniya inda take sa ran za ta ci bashin akalla dala biliyan 14.4 (kimanin Naira Tiriliyan 5.993) domin yin wasu ayyukan layin dogo.
Tuni dai rahotanni suka ce Bankin Standard Chartered ya amince da bayar da lamuni na dala biliyan 3.02 (N1,256tr) don gudanar da ayyukan. Alamu na nuni da cewa irin wannan matakin na iya rage cin bashi daga Sin
Asali: Legit.ng