Sojoji sun sake samun gagarumin nasara kan Boko Haram, mayaka da iyalansu 41 sun mika wuya a Borno
- Rundunar sojojin Najeriya ta ce mayakan Boko Haram da iyalansu 41 sun mika wuya a kauyen Dissa da ke Jihar Borno
- Yan ta'addan sun mika wuya ne a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu
- Wadanda suka yi sarandan sun hada da maza 11, mata 22 sai yara takwas
Borno - Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun sake samun gagarumin nasara a kokarinsu na kakkabe yan ta’adda da miyagu a yankin arewa maso gabashin kasar.
A yanzu haka, mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram da iyalansu 41 sun mika wuya a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu.
A wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na Twitter a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu, ta bayyana cewa wadanda suka mika wuya sun hada da maza 11, mata 22 sai yara takwas.
Ta kuma bayyana cewa dakarun Bataliya ta 144 da ke kauyen Dissa na Jihar Borno ne suka amshe su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rundunar sojin ta rubuta sanarwar kamar haka:
"Aikin kakkaba da ke gudana a yanzu ya sake samun gagarumin nasara yayin da mayakan Boko Haram da iyalansu 41 da suka hada da maza 11, mata 22 da yara 8 sun mika wuya ga dakarun Bataliya ta 144 da ke kauyen Dissa na jihar Borno a ranar Litinin, 21 ga watan Fabrairu.”
Sama da yan Boko Haram/ISWAP 30,000 sun mika wuya, Gwamna Zulum
A wani labari makamancin wannan, mun kawo a baya cewa Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnati ta samu yan ta'addan Boko Haram da ISWAP 30,000 da suka mika wuya daga Satumba 2021 kawo yanzu.
Gwamnan ya kara da cewa ba wai suna mika wuya don wani alkawarin kudi ko dukiya bane, suna yi don kansu ne.
Zulum ya tabbatar da cewa nan da lokacin zaben 2023 rikicin Boko Haram zata zo karshe a Najeriya.
Asali: Legit.ng