Yanzu-yanzu: Gwamnonin APC sun shiga ganawar gaggawa da Shugaba Buhari
- Gwamnonin jam'iyyar APC suna ganawa da Buhari kan yanke shawara kan lamarin zaben shugabannin jam'iyyar
- Wannan ya biyo bayan ganawar da Gwamnonin sukayi daren Litinin a gidan Gwamnan Kebbi
- Matasan jam'iyyar sun yi All-wadai da dage taron gangamin da akayi zuwa watan Maris
Shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka ya shiga ganawar gaggawa da gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a dakin taron fadar Shugaban kasa Aso Villa, Abuja.
Wadanda ke hallare a ganawar sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da wasu gwamnoni 18, rahoton DailyTrust.
Daga cikin gwamnonin akwai na Yobe, Kano, Kogi, Ekiti, Nasarawa, Kwara, Ebonyi, Jigawa, Lagos, Imo, Ogun, Borno, Niger, Gombe, Osun, Kebbi, Plateau, da kuma mataimakin gwamnan Anambra.
Ana zaman ne bisa dage taron gangamin jam'iyyar da Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, yayi wanda ya bar baya da kura.
An shiga zaman ne don Shugaba Buhari ya amince da sabbin tsare-tsaren da aka yi da kuma tattauna yankunan da za'a baiwa matsayi.
Ana sa ran Shugaba Buhari zai kwantar da kuran saboda gudun rugujewar jam'iyyar.
Dalilin jinkirta taron gangamin APC: Tsohon gwamna ya ce Buni ne ya jawo, yana son ya gaji Buhari a 2023
Wani tsohon gwamnan wanda ya kasance cikin wadanda suka kafa jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya zargi Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe da son a yi taron gangamin jam’iyyar da zaben fidda gwanin shugaban kasa na 2023 a rana guda.
Dalilin jinkirta taron gangamin APC: Tsohon gwamna ya ce Buni ne ya jawo, yana son ya gaji Buhari a 2023
Da yake martani kan rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar mai mulki kan taronta, tsohon gwamnan ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta daukar mataki saboda ra’ayin APC, Daily Trust ta rahoto.
Bayan an kai ruwa rana, jam’iyyar mai mulki ta sanar da ranar 26 ga watan Maris a matsayin ranar babban taronta na kasa.
Asali: Legit.ng