An gurfanar da mata 3 kan laifin jika AlKur'ani da jinin biki da jefawa cikin masai a Zamfara

An gurfanar da mata 3 kan laifin jika AlKur'ani da jinin biki da jefawa cikin masai a Zamfara

  • Ana zargin wasu mata uku da laifin wulakanta Alkur'ani a jihar Zamfara kuma an damkesu
  • An yi zargin wani Malamin tsubbu mai suna Tukur ne ya sanyasu wannan mumunar aiki
  • Lauyan gwamnati ya gabatar da AlKur'anin da suka wulakanta gaban Alkali

Bungudu, jihar Zamfara - An gurfanar da wasu mata uku gaban kotun Shari'a dake Gusau, birnin jihar Zamfara kan zargin laifin wulakanta littafin Al-Qur'ani mai girma.

Matan da ake tuhuma sun hada da Rabi Bello, Hazira Bello da Hafsatu Isah, duka yan garin Gada na karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Matan sun gurfana gaban Alkali Garba Sahabi Gusau.

Zamfara
An gurfanar da mata 3 kan laifin jika AlKur'ani da jinin biki da jefawa cikin masai a Zamfara
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bayan watanni 11, Iyalan yan kasuwa canjin Kano da DSS ta kama sun ga mazajensu

Ana zarginsu da laifin jika AlQur'ani mai girma da jinin biki, sannan suka jefar cikin masai, rahoton Daily Trust.

A cewar rahotanni, hujjojin da aka gabatar gaban kotu sun hada da AlQura'ni guda jike da jini, sirinjin jinin biki 77 da aka dauka bayan haihuwa, wasu littafai, takarda mai dauke da sunan daya cikin matan da kuma wasu abubuwan tsubbu da boka mai suna Tukur ya basu.

Lauyan hukuma ya bayyanawa kotu cewa matan na kokarin sihirin neman kudi ne.

Alkalin ya dage zaman zuwa ranar 3 ga Maris.

Kano: 'Yan sanda sun damke matashin da ya yaga Qur'ani tare da taka shi

Wani matashin maigadi wanda har yanzu ba a san sunansa ba, ya na hannun hukumar 'yan sanda ta jihar Kano kan zarginsa da ake yi da yaga Qur'ani tare da take wani sashinsa.

Wanda ake zargin, ya kubuta daga babbaka shi da ranshi da jama'ar yankin Kuntau a birnin Kano suka yi niyya bayan isar jami'an hukumar Hisbah wurin.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta amince da bukatar NDLEA kan Abba Kyari da sauran mutum 6

Daga bisani jami'an Hisbah sun mika shi hannun 'yan sanda kuma a halin yanzu an tsare shi inda ake cigaba da bincike.

Wani dan uwan mamallakin gidan da matashin ke gadi mai suna Sunusi Ashiru, ya sanarwa da Daily Trust cewa an tabbatar masa da kyar matashin ya kubuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng