Borno: Hotunan yadda sojoji suka gargaji tarin 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP

Borno: Hotunan yadda sojoji suka gargaji tarin 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP

  • Rundunonin sojin Najeriya a jihar Borno sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama a wasu yankunan jihar
  • Hakazalika, majiya ta shaida cewa, rundunar ta kuma kwato kayayyakin aikata barna daga hannun 'yan ta'addan
  • Lamarin ya faru ne a jiya Litinin 21 ga watan Fabrairu, kamar yadda wata sanarwar soji ta fitar ta kafafen sada zumunta

Jihar Borno - Rundunonin sojin Najeriya, sun yi aikin share fage a wasu sassan jihar Borno, sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a yayin aikin.

Rundunar 402 SF Brigade, a ranar 21 ga watan Fabrairu ne ta ragargaji 'yan ta'adda da dama a yankin Timbuktu Triangle a jihar Borno, inda ta kwato makamai da yawa ciki har da bama-bamai.

Yadda sojoji suka ragargaji 'yan ta'adda a Borno
Borno: Hotunan yadda sojoji suka gargaji mafakar 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP | Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

A bangare guda, rundunar 26 Task Force Brigade ta yi aikin sintiri tare da share maboyar 'yan ta'addan, lamarin da ya kai ga janyewar ISWAP/Boko Haram daga yankunan Fadagwe na da kewaye na jihar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ISWAP da Boko Haram a Adamawa

Sanarwar daga rundunar sojin Najeriya

Wata sanarwa da rundunar sojin Najeriya ta fitar a shafinta na Twitter ya bayyana yadda lamarin ya faru, kana sanarwar na dauke da hotunan kayayyakin da aka kwato.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce:

"A ci gaba da gudanar da ayyukan share fage da mamaye fagen daga na NA, sojojin rundunar 402 SF Brigade a jiya 21 ga watan Fabrairun 2022 sun kashe 'yan ta'addar ISWAP/BHT da dama a Timbuktu Triangle a jihar Borno. Sojojin sun kwato manya-manyan makamai, bama-bamai, Mowag APC guda 1, TCV guda 1 da dai sauransu.
"Hakazalika, rundunar 26 Task Force Brigade ta gudanar da aikin share fage da sintiri a kauyen Fadagwe da matsugunan da ke makwabtaka da jihar Borno. 'Yan ta'adda sun janye cikin firgici saboda karfin wuta da sojoji suka yi. An samu nasarar kwato motoci da dama na 'yan ta'addan."

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kashe Buba Danfulani da kwamandojin ISWAP 4 a Sambisa

Kalli hotunan:

Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda a cikin 'yan kwanakin nan, musamman a jihar Borno.

Sojin Najeriya sun ragargaji 'yan ISWAP da Boko Haram a Adamawa

A wani labarin, rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa, ta ragargaji wasu 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP da ke kokarin janyewa juna bayan ba hammata iska a wani yankin jihar Adamawa.

Rundunar sojin ta ce ta samu rakiyar 'yan sa kai na Civilian JTF, inda ta samu bayanai na sirri kan motsin 'yan ta'addan da ya kai ga nasarar hallaka wasu a yau Litinin 21 ga watan Fabrairu.

Rundunar ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne jim kadan bayan da 'yan ta'addan suka ba hammata iska, inda suke kokarin janyewa juna bayan fafatawarsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Tags: