Wawure kudin kasa: Kotu ta tasa keyar tsohuwar minista da wasu mutane 2 zuwa gidan yari
- Babbar kotun tarayya da ke zama a garin Jos, ta yanke wa tsohuwar ministar albarkatun ruwa, Sarah Ochekpe, daurin shekaru shida a gidan gyara hali
- Alkalin kotun, Justis Musa Kurna ya kuma yankewa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a jihar, Raymond Dabo, da Evangelist Leo Sunday Jitung, daurin watanni uku kowannensu
- Tsawon shekaru hudu kenan suna fuskantar shari'a kan zargin wawure kudin kasa
Plateau - Wata babbar kotun tarayya da ke zama a garin Jos, babbar birnin jihar Filato, ta yankewa tsohuwar ministar albarkatun ruwa, Sarah Ochekpe, daurin shekaru shida a gidan yari kamar yadda shafin EFCC ta rahoto.
Kotun ta kuma yankewa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar, Raymond Dabo, da Evangelist Leo Sunday Jitung, daurin shekaru shida kowannensu.
Mai shari’a, Justis Musa Kurna ne ya zartar da hukuncin a ranar Talata, 22 ga watan Fabrairu.
Su duka ukun sun shafe tsawon shekaru hudu suna fuskantar shari’a kan zargin hada kai da kuma wawure kudaden kasa, rahoton Daily Trust.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kotun ta same su da laifi a kan tuhume-tuhume na daya da na biyu kan hada baki da kuma rike kudi naira miliyan 450 wanda ya haura adadin da doka ta tanada.
Kotu ta kuma sallame su da wanke su a kan tuhuma na uku.
Sai dai kuma, an tattaro cewa an basu zabi biyan tarar naira miliyan daya.
Kotu ta amincewa NDLEA ta ci gaba da tsare abokan harkallar Abba Kyari 2
A wani labarin, wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amince da bukatar hukumar NDLEA na neman izinin ci gaba da tsare wasu mutum biyu da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi tare da Abba Kyari.
Mai shari’a Zainab Abubakar ta bayar da umarnin a tsare Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus na tsawon kwanaki 14 a cibiyar NDLEA da ke Abuja kafin a gudanar da bincike, inji rahoton The Nation.
Mai shari’a Zainab Abubakar ta ba da wannan umarni ne bayan ta saurari shugaban lauyoyin NDLEA, Joseph Sunday wanda ya nemi a ci gaba da ajiye mutanen.
Asali: Legit.ng